‘Yan Nijeriya da dama na ci gaba da kokawa kan karin farashin iskar gas na LPG wanda ake amfani da shi wajen dafa abinci, duk da matakan da gwamnati ta dauka.
Wasu mazauna babban birnin tarayya Abuja, wadanda suka zanta da kamfanin dillancin labaran Nijeriya (NAN) a ranar Lahadi a Abuja, sun jaddada bukatar da yake akwai a kan gwamnati na ta gaggauta magance tsadar iskar gas din.
- Maulidi: Fityanul Islam Ta Jajanta Wa Al’ummar Borno Kan Ibtila’in Ambaliyar Ruwa
- Anya Barcelona Za Ta Iya Kai Bantenta Kuwa A Gasar Zakarun Turai Ta Bana?
Wannan a cewarsu zai taimaka wajen rage wasu kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.
NAN ta ruwaito cewa ana siyar da duk kilogiram daya (1kg) na iskar gas a tsakanin N1,300 zuwa N1,400 ya danganta da wuri da zaka siya, kuma cika silinda mai nauyin kilogiram 12.5 a yanzu yana kai wa N16,000 zuwa N17,000 sabanin N12,500 zuwa N13,000 a watan Yuni da Yuli.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Yuni da Yuli, iskar gas din ta ragu zuwa kasa zuwa naira 1,050 kan kowacce kilogiram, amma farashin ya karu a watannin da suka biyo.
Rahoton Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) na baya-bayan nan kan iskar gas na watan Yuli ya nuna cewa matsakaicin farashin dillalan iskar gas din kan silinda mai nauyin kilo 5 ya ragu da kashi 14.23 bisa dari a duk wata daga N6, 966.03 da aka samu a watan Yuni 2024 zuwa N5, 974.55 a watan Yuli 2024.
Haka kuma, matsakaicin farashin dillalan iskar gas na Silinda mai nauyin kilo 12.5 ya ragu da kashi 9.37 a kowanne wata daga N15, 736.27 a watan Yuni 2024 zuwa N14, 261.57 a watan Yulin 2024.
Wata ‘yar kasuwa kuma mahaifiyar ‘ya’ya uku Funke Bamidele ta ce karin kudin iskar gas din girki na daya daga cikin kalubalen da ‘yan Nijeriya ke fuskanta kasancewar shi ne tushen girki a gidaje da dama.
“Mun dauka farashin iskar gas din ya ragu a ‘yan watannin da suka gabata, sai muka sake farkawa zuwa wani karin.
“Iyalai da yawa suna amfani da iskar gas a gidajensu, kuma idan farashin ya ci gaba da karuwa, zai haifar da babban kalubale ga iyalai saboda da kyar muke iya tsira daga wannan mawuyacin halin da tattalin arziki ya fada.
“Man fetur yana da tsada, kananzir na da tsada, dizil yana da tsada, iskar gas yana da tsada. Ya ya gwamnati take son ‘yan Najeriya su rayu?