Bishiyar Kuka na daya daga cikin manyan Bishiyoyin da ake alfahari da su a nahiyar Afirka.
A kiyasin da aka yi, Bishiyar ta kasance guda daga cikin tsoffin Bishiyoyin da ke dadewa a doron kasa, duk kuwa da irin sauyin yanayi da kuma bushewar kasa da ake samu a hamada.
A lokacin damina, Bishiyar ta Kuka na tsotsar ruwa tare kuma da adana shi a jikinta; har zuwa tsawon shekaru tana rayuwa, kazalika tana iya rika tare da adana dubban litar ruwan a tare da ita na tsawon lokaci.
Haka zalika, tana ci gaba da girma har zuwa na mita 30, sannan kuma tana iya shafe shekaru kimanin dubu biyar tana rayuwa.
Sannan, Ganyen Bishiyar na samar da inuwa da abinci da kuma ruwa ga mutane da kuma dabbobi, wanda wannan ne ba bai wa wasu mutane; musamman wadanda ke zaune a hamada damar gina gidajensu.
Bugu da kari, Bishiyar Kuka na dauke da sinadarai masu gina jikin Dan’adam da kuma wasu dabbobin da ke amfani da ita.
Ita kadai ce wadda Ganyenta ke bushewa da kansa a jikin reshenta, yake kuma ci gaba da zama a jikinta har tsawon wata shida.
Kazalika, ana sarrafa ‘ya’yan da suke a cikin kokonta zuwa nau’in alawar da ake sha.
Haka nan, ana kuma shafe shekaru ana amfani da ita wajen sarrafa magunguna da yakar cututtuka da kuma gyran jiki da sauran makamantansu.
Ana kuma amfani da jikinta ana yin igiya tare kuma da amfani da Irinta wajen sarrafa man shafawa.
A bisa wani rahoto da hukumar kula da yanayi ta kasa ta fitar ya nuna cewa, ana kara samun yawan bukatar wannan Bishiyar, domin irin matukar amfanin da take da shi.