Tsohon Gwamnan jihar Imo kuma mai neman tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, Sanata Rochas Okorocha, ya nuna cewa, wasu da dama daga cikin wadanda suka kwashi kudinsu har miliyan dari suka yanki Fom din takara kawai sun yi hakan ne domin fakewa da neman mukamin Ministoci a wajen wanda ya samu nasara.
Sanata Okorocha, wanda ke wakiltar mazabar Imo ta yamma a Majalisar kasa, ya ce kawai wasu din sun sayi Fom din ne domin a tuna da su idan an zo rabon mukaman Ministoci saboda suna sane sarai koda sayen Fom din da suka yi, ba za su iya yin nasarar wajen samun tikitin ba.
Dan majalisar wanda ke magana a cikin wani shirin gidan talejin din TVC a ranar Alhamis, ya kara da cewa, wasu da suka shiga takarar sun yi ne kawai don neman suna da kuma neman dai a dama da su
“Shi ko ka san wasu daga cikin mutanen nan sun sayi Fom din takara ne kawai don a dawo a basu mukaman Ministoci,” ya shaida.
Ya nanata cewar wasu tabbas sun san ba ma za su iya cin zaben cikin gidan ba amma suka dage suka shiga a dama da su.
LEADERSHIP ta rawaito cewa zaben fitar da gwanin Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC dai an ware ranar 6 da 7 na watan June domin gudanar da shi a Abuja inda ‘yan takara 13 za su fafata biyo bayan watsi da mutum 10 da kwamitin tantance ‘yan takara na jam’iyyar ya yi.