Sanata mai wakiltar Neja ta Gabas, Sani Musa, ya ce Babagana Monguno, mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), ya yi murabus saboda tabarbarewar tsaro a kasar.
Musa ya soki hukumar NSA da cewa ba ita ce ta fara sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari barazanar da ‘yan ta’adda ke yi na sace shi ba.
- ‘Yan Bindiga Na Kwararowa Jihata – Gwamnan Nasarawa
- ‘Yan Kannywood Mu Guji Isar Da Sakon Da Bai Dace Ba -Yunusa Gaya
Sanatan yabyi magana ne a ranar Lahadi a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels.
A karshen makon da ya gabata ne wani faifan bidiyo da ‘yan ta’adda suka saki, suka yi barazanar sace Buhari da gwamnan jihar Kaduna, Nasir el-Rufai, ya karade shafukan sada zumunta.
Da yake magana kan lamarin a ranar Laraba, El-Rufai ya ce shugaba Buhari bai san da barazanar sai da ya sanar da shi da kansa.
Musa, wani jigo a jam’iyyar APC, ya ce “bisa dukkan alamu” cewa shugaban kasa ba shi da masaniyar lamarin.
“Idan har gaskiya ne, idan aka yi la’akari da maganar gwamna El-Rufai na cewa shugaban kasa bai sani ba, wannan lamari kadai ya isa a kori NSA.
“Ana kashe mutane a kasa, kuma za ka gaya min cewa a matsayina na shugaban kasa don tsara yadda ya kamata tsaronmu ya kasance, ba ka da masaniya kan haka kuma ba za a iya sanar da shugaban kasa ba. Ya kamata a sallami NSA.”
Da yake karin haske kan matsalar rashin tsaro, Sanatan Neja, ya ce da ya yi murabus idan shi ne NSA na shugaban kasa, inda ya kara da cewa jami’an tsaro a ko da yaushe sun kasa yin aiki da rahotannin sirri.
“Dole ne mu kira. Da ni ne mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro a kasar nan da zan mika takardar murabus dina saboda na gaza. Ba ku jira sai lokacin da aka kawo muku hari sannan za ku yi aiki ba.
“Wadannan bayanan sirrin da ake rabawa bayanai ne da aka ba ku a wani mataki da masu laifin ba su cumma manufarsu da shirinsu ba kuma za ku kawar da su.
“Don haka a gare ni, na yi imani cewa muna bukatar mu sake tsara dabarunmu duba da yawan al’umma. Idan ka je jihar Neja, yau za ka ga ‘yan gudun hijira da dama, mutane sun bar garuruwansu.”
A baya-bayan nan ne mai bai wa shugaban kasa kan sha’anin tsaro, ya ce ‘yan Nijeriya sun gaji da matsalar tsaro a kasar, inda ta kara da cewa ‘yan kasar na kokarin neman taimakon kai.