Ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa ce ranar cika shekaru 75 da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin. Idan muka waiwayi tarihin ci gaban kasar, za mu ga cewa, ta yi aiki tukuru don kara karfinta, duk da cewa tana fama da talauci, da rauni a lokacin kafuwarta, inda ta kafa harsashin masana’antu ta hanyar dogaro da kai, da samun nasarar shiga kasuwannin kasa da kasa ta hanyar hadin gwiwa da bude kofa, sannan ta ci gaba da inganta shirinta na raya kasa, kuma sannu a hankali ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya, bisa la’akari da matsayin GDP. Bayan an takaita tarihin kasar, matakan da ta dauka a kokarin raya kanta kamar ba su da sarkakiya, sai dai kalilan kasashe ne za su iya kiyaye irin wannan ci gaba cikin sauri na dogon lokaci da kasar Sin ta samu. To ko mene ne sirrin kasar Sin a fannin raya kasa?
Idan ka tambayi dan kasar Sin yadda rayuwarsa ta canza a cikin shekaru ashirin da suka gabata ko ma fiye da haka, tabbas zai ambaci abubuwa da yawa: samun karin kudin shiga, da karin abinci masu gina jiki. Kana an samu zama cikin sabbin gidaje masu inganci, yayin da harkar sayayya ta zama mai sauki da ban sha’awa, da dai sauransu, wato dukkan bangarorin suna inganta. Irin wannan ci gaba na hakika da aka samu a cikin rayuwar jama’a, sakamakon ci gaban kasar Sin ne, kuma dalilinsa ne.
- Ambaliya: Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Bai Wa Maiduguri Tallafin Miliyan 20
- Aikin Matatar Mai Na Ya Hana Ni Sayen Arsenal A 2020 – Dangote
Masu mulkin kasar Sin suna da wani muhimmin tunanin da ake kira “Mai da jama’a a gaban komai.” A nasu ra’ayin, kasa tana bauta wa al’umma, kuma dalilin da ya sa ake neman ci gaban kasa shi ne don baiwa al’umma damar rayuwa mai inganci. Wannan ra’ayi ne da ya sa al’ummar kasar Sin kokarin hadin kai da juna, ta yadda siyasar kasar ta tabbata. Mutane sun yi imanin cewa rayuwarsu za ta kara kyau a nan gaba, kuma kokarin aiki zai haifar da sakamako mai gamsarwa. A sakamakon haka, ana bin dokoki, ana aiwatar da manufofi, ana kokarin cimma burikan da aka sanya daya bayan daya.
Da an ji batun “Mai da jama’a a gaban komai”, za a ga tamkar babbar magana ce, amma ana iya ganin misalan aiwatar da hakan a ko ina a kasar Sin: A kasuwannin birnin Beijing, sau da yawa na sayi kayayyakin nau’in “kau da talauci da taimakon manoma”(gwamnati na taimakawa yankunan da suke da koma baya ta fuskar tattalin arziki wajen bunkasa sana’o’i. Inda ta hanyar kera wasu kayayyaki na musamman, ana raya masana’antun da za su iya samar da kudin shiga, don tabbatar da ci gaban tattalin arziki da karin ayyukan yi). A gundumar Chun’an da ke lardin Zhejiang na kasar Sin, na ga yadda aka tsara kauyuka bisa yanayin albarkatunsu, don raya wasu sana’o’i daban-daban, kamar kera magungunan gargajiya, da bunkasa ayyukan gona ba tare da gurbata muhallin halittu ba, da kiwon kifi, da yawon bude ido, da dai sauransu, ta yadda aka samar da isassun damammaki ga mazauna kauyukan domin su wadata. Kana a tashar jiragen ruwa ta garin Ningbo, dake gabashin kasar Sin, na ga sabbin fasahohi da ke baiwa ma’aikata damar zama a ofisoshi, da sarrafa injuna masu kwashe kwantenoni ta na’urorin da ake sarrafawa daga nesa, ta yadda ba za su ci gaba da shan wahalar aiki a karkashin zafin rana ba. Ban da haka, ana ci gaba da kokarin gina layukan dogo masu inganci a tsakanin biranen kasar Sin, lamarin da ke baiwa jama’a sauki wajen yin balaguro a kasar…
A halin yanzu, yayin da hadin gwiwar Sin da Afirka ke ci gaba da zurfafa, ana tabbatar da manufar “Mai da jama’a a gaban komai” a dimbin ayyukan da suke amfanar da jama’ar Sin da Afirka. Misali, a birnin Lagos na Najeriya, layin dogo na Blue Line da wani kamfanin kasar Sin ya gina, ba kawai yana saukaka tafiye-tafiyen jama’a ba, har ma ya samar da taimako a fannin rage cunkoso a cikin gari. Yana kuma rage fitar da gurbataccen hayaki, da samar da ayyukan yi ga daruruwan mutane.
A kauyuka da dama na Najeriya kuwa, kamfanonin kasar Sin sun samar da tashoshin wayar salula masu amfani da makamashin hasken rana, lamarin da ya bai wa fiye da mutane miliyan 7 dake yankunan karkara damar yin amfani da yanar gizo ko intanet. Kana a kasar Kenya, nau’in shinkafa da kwararrun masanan ilimin aikin gona na kasar Sin suka samar, ya sa yawan shinkafar da ake samu ta karu matuka, a lokacin da ake gwajin nomanta, wanda hakan ya baiwa kasar damar samun isashen abinci bisa dogaro da kai. Ban da haka, cibiyoyin koyar da ilimin sana’a na “Luban Workshop” guda 17 da kasar Sin ta kafa a sassan kasashen Afirka, sun samar da fasahohin sana’o’i da guraben aikin yi ga dubun dubatar matasan Afirka…
Idan manufar “Mai da jama’a a gaban komai” ita ce “Sirrin” ci gaba mai dorewa na kasar Sin, to, Sin ta raba wa kasashen Afirka wannan muhimmin sirrinta. A gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a baya-bayan nan a birnin Beijing na kasar Sin, kasar ta ba da shawarar yin aiki tare da kasashen Afirka wajen zamanintar da kansu, da mai da kare moriyar jama’a gaban duk wani aiki na daban. Ta haka, babu shakka, al’ummar kasashen Afirka za su samu karin fa’ida, wadda kuma za ta zama tushen ci gaban tattalin arzikin Afirka. (Bello Wang)