Wasu makiyaya guda shida sun rigamu zuwa gidan gaskiya a yayin da wasu karin bakwai suka bace bat a kauyukan Mongi da Langai da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato.
Shugaban kungiyar Fulani (MACBAN) a jihar Filato, Malam Nura Abdullahi shi ne ya tabbatar da hakan, ya yi zargin cewa wasu mambobin kungiyar ‘yan banga da ke Bauchi ne a ranar 22 ga watan Yulin 2022 suka shiga cikin kauyukan tare da kama Fulanin hadi da kai su daji da kashe su.
- Matsin Rayuwa: Za A Rage Farashin Man Fetur A Afrika Ta Kudu
- NDLEA Ta Kwace Tiramol Miliyan 2.7 A Legas
Shugaban na MACBAN ya kara da cewa mambobinsu Fulani 13 aka kama, inda aka samu gawar shiga daga cikin yayin da bakwai kuma ba a san inda suke ba har yanzu.
Ya ce, “Daga ranar Lahadi 23 ga watan Yuli zuwa ranar Lahadi 31 ga watan Yuli mun binne mutum shida. Dukkanin wadanda aka kashe ba su san hawa ko sauka ba. Sannan har yanzu hudu kuma sun bace.
“Biyu daga cikin wadanda aka kashe sun fito ne daga Mongi sai kuma hudu ‘yan kauyen Langai. Daga cikin cikin wadanda aka kashe ya kammala jami’a sai kuma a cikinsu akwai dan shekara 65 dukka an kashe ba tare sun yi laifin komai ba.
“Wannan ba abu ne da za a lamunta ba. Ta’addanci ne marar dadi. Daukan hukuncin kisa lallai ba abu ne da ya kamata jama’a suke yi ba. Idan ana zarginsu da laifin garkuwa da mutane, kamata ya yi a kaisu kotu ta bincika ta hukuntasu ba wai wadanda suka kama su din su zartar musu kawai da hukuncin kisa ba.
“Ya kamata ne kotu ta bincika ta tabbatar da abun da ake zarginsu kafin a kai ga yanke musu hukunci.
“Bayan da aka kashe, wadanda suka kashe su din sun sace musu kadarorinsu da kudadensu. Sun kwashe musu Mashina. Muna kira ga hukumomin tsaro da su dauki mataki kan wannan lamarin. Na kuma sanar da GOC 3 Division kan wannan batun.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya ce rundunar su tana sane da faruwar lamarin sai dai kisan ya faru ne ba a karkashin ikonsu ba.
Ya ce, “Ban san cikakken abun da ya faru ba. Ina tunanin rundunar ‘yan sandan reshen jihar Filato ne suke da alhakin yin magana kan abun da ya faru.
“Ba mu da masaniya kan kungiyar da suke zargi. Idan sun san mutunan da suka kashe musu mambobi su nuna mana su. Don an ajiye gawarwakin wadanda aka kashe a Bauchi ba shine yake nufin an kashe a Bauchi ba ne.”