An sallami jami’in Sojan ruwa, Abbas Haruna daga aiki wanda aka tsare tun shekarar 2018 bisa umarnin wani Birgediya, ya samu ‘yanci bayan shafe shekaru shida a garƙame.
Duk da dokar sojojin Najeriya ta 2004 ta ƙayyade hukuncin rashin biyayya zuwa shekaru biyu, Haruna ya zauna a tsare har na tsawon lokaci mai yawa, lamarin da ya haifar da kiraye-kiraye daga mutane da kuma sanya baki daga kwamitin majalisar wakilai kan Sojojin ruwa.
- Sojoji Sun Kama Sojan Da Ya Kashe Mai Zanga-zanga A Kaduna
- Kasar Sin Za Ta Sanya Takunkumi Kan Kamfanonin Sojan Amurka Wadanda Suka Sayar Da Makamai Ga Yankin Taiwan
Shugaban Brekete Family, Ordinary Ahmed Isah, ne ya sanar da sakin Haruna, inda ya ce yayin da aka sako shi, an kuma sallame shi daga aikin Sojin ruwa. Matar Haruna, Hussaina Iliyasu, ta bayyana yadda rikicin ya fara bayan wani saɓani yayin aikin musamman a jihar Taraba.
A yayin shirin Brekete Family, Hussaina ta nuna farin cikinta kan sakin mijinta duk da ƙalubalen da ke gaba bayan sallamarsa daga aiki.
Yanzu abin jira a gani shi ne sakamakon binciken da rundunar tsaro ta ce za ta yi dangane da batun. Janaral Christopher Musa ya sha alwashin yin bincike kan wannan batu.