Hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna masu dauke da mutane a sararin samaniya ta kasar Sin ko (CMSA), ta kaddamar da tsarin rigunan da ‘yan saman jannatin kasar za su sanya, a lokacin da za su gudanar da ayyukan bincike a duniyar wata. A yau Asabar ne aka kaddamar da rigar, tare da neman shawarar sunan da za a baiwa rigar daga jama’a.
An nuna rigar ne a wani bikin dandalin fasahohi masu alaka da tufafin da ‘yan saman jannati suke sanyawa karo na 3, wanda cibiyar gudanar da bincike, da horar da ‘yan sama jannati ta kasar Sin ta gudanar, a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar Sin.
‘Yan sama jannatin kasar Sin Zhai Zhigang, da Wang Yaping, sun sanya sabuwar rigar mai launin fari da jajayen ratsi, don nuna tsarinta a cikin wani bidiyon da aka watsa a wajen bikin. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp