Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nada Hauwa Isah Ibrahim a matsayin sabuwar manajan daraktan gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV).
Nadin nata na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimakawa manajan, jamilu Lawan Yakasai ya fitar.
- Hanyoyi 13 Na Ladabtar Da Mata Ba Tare Da Duka Ko Zagi Ba
- Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Al’ummun Duniya Sun Nuna Karin Amincewa Da Kasar Sin
Ya tabbatar da nadin Hauwa Isa Ibrahim matsayin Manajan Darakta ta gidan rediyo da talabijin na Abubakar Rimi daga oshishin Gwamna.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Mayun da ya gabata ne Gwamnan ya amince da nadin Hajiya Hauwa Isah Ibrahim a matsayin mukaddashiyar shugabar gidan rediyo da talabijin na ARTV, biyo bayan dakatarwar da aka yi wa tsohon shugaban, gidan Mustapha Adamu Indabawa.
An dakatar da shi ne sakamakon zargin da Hukumar Karbar Korafe-Korafe da Hana Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano ke masa.
Gwamnan kuma ya amince da nadin Idris Abba a matsayin mataimakin Manajan Darakta na gidan.