Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Ga Gwamanatin Tarayya A Kan Tozarta Marasa Lafiya Daga Jami’an FIRS A Kano
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu!
Cikin girmamawa gare ku shugabanni da Jami’o’in Lafiya na ƙasata baki ɗaya.
Na ɗauki alƙalamina ne domin na kiraye ku a kan wani ganganci da kan tafi da rayukan al’umma da na ga hukumar haraji ta Nijeriya (FIRS) ta yi a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Kano, wato ‘Best Choice Specialist Hospital’ da ke unguwar Gadon Ƙaya kan shataletalen Tal’udu.
Wasu daga cikin marasa lafiya da wasu iyaye sun kawo wa jaridar Alfijir labarai ƙorafi a kan yadda jami’an hukumar tattara harajin suka zo tare da jam’ian tsaro da bindigogi suna musu barazana a kan sai dole sun tashi sun fita daga cikin asibitin bayan bala’in da suke ciki na rashin lafiya, ga shi kuma sun yi yawo wurare da dama a Kano sun rasa inda za a iya samun gadon kwanciya musamman a ɓangaren larurar da ta shafi yara da jarirai sai nan ɗin!
Babban abin takaicin ma shi ne wasu daga cikin likitoci da ke Kano da ma wasu jahohin sun tsunduma yajin aiki a kan haƙƙoƙinsu, maimakon hukumar ta yi aiki da hankali wajen taimaka wa al’umma domin jin-ƙan su, a’a sai ƙoƙari take wajen ƙara nakasa rayuwar waɗannan marasa lafiyar da ke asibitin ko kuma ma hallaka su!
Matsalar haraji da ke tsakaninku da asibiti matsala ce da ta shafe ku, ba abin da ya shafi waɗanda suka zo neman lafiya asibitin ba ne.
Don haka muke kira ga shugabanni na wannan ƙasa tamu mai albarka, da hukumar kare haƙƙin bil’adama kan wannan cin zarafin da aka yi wa al’umma da a kawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Ku kuma hukumar tattara haraji, ku dubi Allah ku canja hanyar da za ku bi wajen neman haƙƙinku, don inda haƙƙinku ya ƙare nan fa na wasu ya fara.
Idan da ƴaƴanku ne ke zuwa asibitin ba na talakawa ba, da ai ba za ku yi hakan ba!
Kukan Kurciya Jawabi Ne!
Daga
MUSA BESTSELLER, EDITAN JARIDAR ALFIJIR LABARAI
Mai Biyayya A Gare ku