Baban mai taimakawa shugaban ƙasa akan harkokin siyasa Hon. Ibrahim Kabir Masari ya bayyana dalilan da yasa suka shiga suka fita shi da gwamna Dikko Raɗɗa a kasoke aikin sake gina hanyar kankara zuwa Katsina daga hannun ɗan kwangilar.
Ibrahim Kabir Masari ya yi wannan kalamai ne a Katsina a lokacin bikin raba shinkafar da gwamnatin tarayya ta baiwa jihar Katsina domin rabawa al’umma su rage raɗaɗin rayuwa da ake fama da shi.
- Tinubu Zai Wuce Faransa Daga Birtaniya
- Yadda Muka Sanya Tinubu Ya Soke Kwangilar Aikin Hanyar Kankara Zuwa Katsina – Ibrahim Masari
Wannan aikin hanyar mai tsawon kilo mita 170 da ta taso daga marabar kankara zuwa Katsina ta haɗa ƙananan hukumomi bakwai da yawansu manoma ne sannan suna fuskantar matsalar tsaro daga ‘yan bindiga
Kamar yadda alkaluma suka nuna aikin wannan hanya sai ratsa kananan hukumomi guda 7 da suka haɗa da Malumfashi da Kankara da Ɗanmusa da Safana da Dutsinma da Kurfi da kuma Ɓatagarawa a jihar Katsina.
Lokaci da aka bada aikin wannan hanya al’umma da dama sun nuna farin cikin su da samun wannan aiki wanda suka bayyana cewa zai taimakawa al’umma musamman manoma sannan zai taimakawa jami’an tsaro wajen kai ɗauki a ya yin da aka kai hari wuce gona da iri.
Sai dai kwatsam aka ji labarin ministan ayyuka na Najeriya ya soke wannan kwangila daga hannun kamfanin da aka baiwa ita daga farko duk da cewa an fara aikin.
Shima a nasa jawabin baban mai taimakawa shugaban kasa a harkokin siyasa Hon Ibrahim Masari ya bayyana wasu hanyoyi da gwamnatin tarayya ta bada aikin su, sai dai ya ce hanyar kankara zuwa Katsina ba a ɗora ƙwarya a gurbin ta ba shi yasa suke je wajen shugaban ƙasa domin ya soke ta.
Ana dai zargin cewa wani jigo ne a jam’iyar PDP a Katsina kuma ɗaya daga cikin yaran Ministan Abuja Nyesom Wike aka baiwa kwangilar aikin hanyar tun farko, lamarin da bai yi masu daɗi ba, inda suka shiga suka fita aka dakatar da aikin, wanda yanzu ba a san matsayin da aikin hanyar yake ciki ba.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko shugaban ƙasa zai sake bada aikin hanyar a wani kamfanin da gwamna Dikko Raɗɗa da Hon. Ibrahim Kabir Masari suke so ko kuwa shikenan ruwa ta sha?