Mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta yi alkawarin inganta rayuwar al’ummar karkara, yayin da ta kaddamar da yakin neman zabe a karamar hukumar Kagarko gabanin zaben kananan hukumomin jihar a ranar 19 ga watan Oktoba.
Dakta Sabuwa, a wajen gangamin yakin neman zaben, ta bukaci al’ummar yankin da su zabi Muhuyideen Abdullahi Umar na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin shugaban karamar hukumar.
- An Kashe Dorinar Ruwa A Jihar Kebbi Bayan Ta Kashe Mai-Gadin Lambun Basarake
- Darajar Masana’antun Samar Da Kayayyakin Sadarwa Na Laturoni Ta Sin Ta Karu Da 13.1% A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Ta kuma bada tabbacin ci gaba da ayyukan more rayuwa a karkara da Gwamnatin Sanata Uba Sani ke yi cikin hanzari, idan har aka zabi dukkan ‘yan takarar shugabannin kananan hukumomi da kansilolin APC a shiyyar baki daya.
Dan Takarar Shugabancin Kagarko, Hon. Muhuyideen Umar wanda malami ne a Sashen Tarihi na Jami’ar Jihar Kaduna, ya ce, idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta aiwatar da tsarin gudanar da mulki na bai daya, domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, inda za a samar wa matasa da mata da sana’o’in dogaro da kai.
Mataimakiyar Gwamnan, ta kuma bai wa ‘yan takarar Kansiloli tutar tsayawa neman zabe a jam’iyyar APC da suka fito daga unguwanni 10 da ke karamar hukumar.