Samar da ci gaban rayuwa buri ne na daukacin bil adama. Kaza lika, daya ne daga muhimman ginshikai da daukacin kasashen duniya ke fatan cimmawa, kuma manufa ce da ba a kawo karshenta a tsawon tarihin rayuwar dan Adam a doron kasa.
Tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarar nan ta raya ci gaban duniya wato “Global Development Initiative” ko GDI a takaice, yayin zaman muhawara na babban taron MDD karo na 76 a watan Satumban shekarar 2021, Sin ta ci gaba da samar da gudummawa bisa basirarta da karfinta na tunkarar batutuwan ci gaban kasa da kasa. A bana shekaru 3 ke nan bayan gabatar da wannan shawara ta GDI, kuma har yanzu ana ta kokarin karfafa matakan cimma nasararta.
- Sin Ta Harba Tauraron Dan Adam Mai Nazarin Duniyar Dan Adam
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Kwamitin Kasa Na Shirya Liyafar Karrama Gwaraza A Fannin Raya Alakar Sin Da Amurka
Baya ga kasar Sin da ta gabatar da shawarar GDI, sassan kasa da kasa na ci gaba da rungumar shawarar, kawo yanzu kasashe da hukumomin kasa da kasa da suka nuna goyon bayansu ga wannan shawara sun haura 100, suna kuma ci gaba da karuwa, baya ga kasashe sama da 80 da suka shiga kawancen tabbatar da nasarar wannan shawara.
Masharhanta na jinjinawa kwazon kasar Sin bisa aiki da take yi tukuru tare da sauran abokan tafiya, musamman ganin yadda karkashin wannan shawara ta GDI, Sin ke ta fadada zuba jari ga ayyukan da suka shafi shawarar, inda adadin ayyukan bunkasa ci gaban duniya masu nasaba da ita suka zarce 1,000. Baya ga hakan, mun ga yadda Sin ta aiwatar da wasu ayyuka na hadin gwiwa tsakanin sassa 3, wato Sin da daidaikun kasashe, da kuma wasu hukumomin kasa da kasa da yawansu ya haura 140, ayyukan da aka gudanar da su a sama da kasashe 60.
Baya ga haka, kasar Sin ta samar da cibiyoyin horas da fasahohin kere-kere masu dacewa da aikin ingiza shawarar ta GDI, don baiwa dimbin al’ummun duniya damar cin gajiyar shawarar a kasashe masu tasowa. Bisa wannan shiri, an bude cibiyoyin koyar da sanin makaman aiki sama da 1,000 a irin wadannan kasashe, inda tuni kwararru sama da 40,000 suka ci gajiyar horo daga wadannan cibiyoyi.
Yayin da shawarar GDI ke samun tagomashi tsakanin sassan kasa da kasa, kuma take kara zurfafa hadin gwiwa da dukkanin sassa wajen yayata cin gajiya daga gare ta, ko shakka babu duniya za ta ci gaba da more damammakin zamanintarwa irin na kasar Sin, a daya hannu Sin da sauran sassan duniya za su ci gaba da dunkule wajen raba gajiyarsu.
Fatan dukkanin sassan kasa da kasa dai shi ne shawarar GDI, da makamantanta za su ci gaba da cimma nasara, su kuma dunkule tare da manyan manufofin bunkasa duniya, irinsu ajandar wanzar da ci gaba ta MDD ta nan zuwa shekarar 2030, da ajandar bunkasa kasashen Afirka ta kungiyar AU ta nan da shekarar 2063 da sauransu, ta yadda kasar Sin da sauran sassan kasa da kasa, za su kai ga kara ingiza ci gaban duniya bisa daidaito, da adalci, har a kai ga gina duniya mai makomar bai daya ga daukacin bil Adama.(Saminu Alhassan)