Kimanin mata da yara kanana 1,000 da ke bukatar kulawa ta gaggawa, nan ba da jimawa ba za a kwashe su daga Gaza zuwa Turai, in ji shugaban hukumar lafiya ta duniya (WHO) a Turai, Hans Kluge a wata sanarwa a ranar Litinin.
Kluge ya ce a cikin wata hira da ya yi da AFP cewa, Isra’ila “ta shirya fitar da karin mabukata kulawar gaggawa su 1,000 nan gaba kadan zuwa Asibitoci a Tarayyar Turai”.
- NDLEA Ta Kama Kwayoyin Fiye Da Naira Biliyan 7 A Tashar Ruwa Ta Apapa Da Onne
- Xi Ya Jaddada Bukatar Ingiza Bude Kofa A Matsayin Koli Domin Cimma Nasarar Sauye Sauye Da Samar Da Ci Gaba
Ya kara da cewa, WHO wadda ita ce hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, da kasashen Turai za su taimaka wajen kwashe mutanen daga Gaza.
Masu bincike na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Alhamis sun zargi Isra’ila da kai wa cibiyoyin kiwon lafiya hari da gangan a Gaza, da kuma kisa da azabtar da ma’aikatan kiwon lafiya a Gaza. WHO na zargin Isra’ila da “laifin take hakkin bil’adama”.
Wakilin WHO a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Rik Peeperkorn a cikin watan Mayu ya ba da sanarwar cewa, kusan mutane 10,000 na bukatar a kwashe su daga Gaza don kula da lafiyarsu cikin gaggawa.
Hukumar WHO ta Turai ta riga ta ba da damar kwashe marasa lafiya 600 daga Gaza zuwa kasashen Turai bakwai tun bayan barkewar yaki tsakanin Kungiyar HAMAS da Isra’ila a watan Oktoban 2023.