Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya soke ziyarar sa zuwa taron Shugabannin Gwamnatocin Ƙasashe rainon Ingila (Commonwealth (CHOGM) na 2024 a Samoa bayan da wani abu ya bugi jirginsa a Filin Jirgin Sama na JFK a New York, wanda ya lalata gilashin kwalkwalwan jirgin.
Kakakin Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa ana gyara jirgin.
- CHOGM 2024: Shettima Zai Wakilci Tinubu A Taron Kasashen Turanci A Birtaniya
- Bunƙasa Tattalin Arziƙi: Shettima Ya Tafi Kasar Sweden Ziyarar Aiki Ta Kwana Biyu
A madadinsa, Shugaba Tinubu ya naɗa wata tawagar ministoci, tare da jagorancin Ministan Muhalli, Balarabe Abbas Lawal, don wakiltar Nijeriya a taron.
Taron CHOGM, wanda ya fara ne tun a ranar 21 ga Oktoba, za a kammala shi a ranar 26 ga Oktoba, 2024.