Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da takaita zirga-zirga a fadin jihar daga karfe 12 na tsakar dare zuwa karfe 6:00 na yammacin ranar Asabar, saboda zaben kananan hukumomi.
Kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye ne, ya bayyana hakan a ranar Juma’a.
- Jirgin Ruwan Aikin Jiyya Na “Peace Ark” Ya Kammala Aikinsa A Benin
- Mai Keta Hakkin Bil Adam Na Ikirarin Kare Shi
Ya bukaci jama’a da su bi dokar don taimakawa wajen tabbatar da zabe na gaskiya.
Gwamnatin tana son ganin an gudanar da zabe cikin ‘yanci, adalci, da lumana.
An hana zirga-zirgar mutane da ababen hawa a dukkanin kananan hukumomi 44 da rumfunan zabe 484 da ke Kano.
Manufar wannan takaita zirga-zirgar ita ce tabbatar da tsaro da kuma samar da yanayi mai kyau don zaben gudanar da zaben gaskiya.
Za a gudanar da zaben a ranar Asabar, 26 ga watan Oktoba.
Sai dai, an bayar da izinin zirga-zirga ga mutanen da ke aikin zabe ko kuma masu ayyuka na musamman.
Dantiye, ya jaddada cewa bin wannan doka yana da matukar muhimmanci don samun nasarar gudanar da zaben kananan hukumomin.