Ƙungiyoyin ma’aikatan jami’o’in Nijeriya da ba malamai ba sun sanar da fara yajin aiki na sai baba-ta-gani daga gobe Litinin, 28 ga Oktoba, saboda rashin biyansu albashi na watanni huɗu tun shekarar 2022.
Wannan sanarwa, da aka fitar yau Lahadi, ta fito daga kwamitin haɗin gwuiwa (JAC) na ƙungiyar ma’aikatan NASU da ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i (SSANU).
- Binciken Ra’ayin Jama’a Na CGTN: Al’ummun Duniya Sun Nuna Karin Amincewa Da Kasar Sin
- Kotu Ta Dakatar da JAMB Daga Hana Ɗalibai Ƴan Ƙasa Da Shekaru 16 Shiga Jami’a
Sanarwar da shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, da Sakatare janar na NASU, Peters Adeyemi, suka sanya hannu, ta bayyana cewa duk da gargadi da zanga-zanga na neman biyansu albashi, gwamnati bata ɗauki wani mataki ba.
“Mun nuna haƙuri mai yawa da kuma dogon lokaci,”
in ji JAC, tare da umartar dukkan mambobinsu a jami’o’in da su gudanar da tarukan majalisarsu shiga yajin aiki, ba tare da wani sassauci ba.