Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba wa Shugaba Bola Tinubu kan kokarinsa na kawo karshen matsalar tattalin arziki da ta addabi Nijeriya.
Ganduje ya bayyana cewa Tinubu ya kawo sauye-sauyen da suka kara wa tattalin arzikin kasa karfi, inda ya bukaci karin goyon baya ga shugaban, musamman daga yankin Kudu maso Yamma.
- Haɓaka Tattalin Arziki Ƙasa: Gwamnan Yobe Ya Bai Wa NEPZA Fili Hekta 300
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Gyara Wutar Lantarkin Arewa Cikin Gaggawa
Ganduje, ya yi wannan kira ne a Akure yayin kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zaben APC na gwamnan Ondo.
“Shugaba Bola Tinubu yana yi wa kasar nan aiki mai kyau. Ya kawo sauye-sauyen da za su inganta cibiyoyinmu don ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin Nijeriya. Muna girmama shi,” Ganduje ya bayyana, inda jaddada rawar da shugaban ya taka wajen ci gaban kasa.
Ganduje, ya yi nuni da cewa tun da Tinubu daga yankin Kudu maso Yamma ya fito, ya kamata a ba shi goyon baya ta hanyar tabbatar da nasarar APC a zaven Ondo.
Ya bukaci mambobin kwamitin yakin neman zaben, wanda Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ke jagoranta, su yi aiki tare don tabbatar da APC a Ondo.
“Dole ne Ondo ta ci gaba da kasancewa a hannun APC ta hanyar dimokuradiyya,” in ji shi.
“Ta yaya za a ce wandonka ya bambanta da rigarka? Sam wannan ba zai yiwu ba. Wannan dama ce a hannun yankinku na siyasa, kuma akwai bukatar a yi abin da ya kamata ta hanyar dimokuradiyya,” in ji shi.
Gwamna Sanwo-Olu, wanda ke jagorantar kwamitin, ya tabbatar wa jama’a cewa yakin neman zaben zai kasance cikin mutunci. Ya lura cewa Gwamna
Sanwo-Olu, yana nuna kwarin gwiwa cewa jam’iyyar APC za ta sake lashe zaben gwamnan a Jihar Ondo a karo na biyu.