Yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na Hadadiyyar Daular Larabawa UAE Mohammed bin Zayed al-Nahyan sun aikawa juna sakon taya murnar cika shekaru 40 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu biyu.
A cikin sakonsa, Xi Jinping ya ce, a cikin wadannan shekaru 40 da suka gabata, huldar kasashen biyu na bunkasuwa yadda ya kamata, kuma a watan Mayun bana, shugaba Al Nahyan ya kawo ziyarar aiki kasar Sin, inda bangarorin biyu suka kai ga matsaya daya kan bunkasuwar huldarsu a nan gaba. Shugaba Xi ya kara da cewa, yana fatan hadin gwiwa da Mohammed al Nahyan wajen kara azama kan raya huldar abota bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni dake tsakanin kasashen biyu, zuwa wani sabon matsayi.
- Mutane Miliyan 33.1 Zasu Fuskanci Ƙarancin Abinci A Nijeriya A 2025
- Hakar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Na Barazana Ga Tsaro – AbdulRazak
A nasa bangaren, Mohammed al Nahyan ya ce, a daidai wannan muhimmin lokaci na cika shekaru 40 da kulla huldar diflomasiyyar kasashen biyu, yana taya Xi Jinping murna da bayyana kyakkyawar fatansa, da fatan kasashen biyu na samun bunkasuwa da wadata da kara hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban.
A wannan rana kuma, firaministocin kasashen biyu, su ma sun aikawa juna sakon taya murna. (Amina Xu)