Asusun lamuni na duniya IMF ya ce, Nijeriya kachokam na biyan basussuka ne da kudaden shigar da taka samu.
A cewar, asusun hakan ne ke janyo rashin samar da kudaden da za a yi amfani da su, wajen gudanar da dimbin ayyukan bunkasa kasa.
- CMG Ta Gabatar Da Shirye-Shiryen Talabijin A Peru
- MDD Za Ta Yi Duk Mai Yiwuwa Wajen Taimaka Wa Nijeriya Kawo Karshen Talauci
Babban Jami’i a sashen tsare-tsare na asusun Dabide Furceri ne ya sanar da hakan a taron manema labarai.
Furceri ya bayyan haka ne, a yayin taron hadaka a tsakanin asusun da bankin duniya da ake ci gaba da yin a karshen shekara a birnin Washington DC.
Kazalika, ya jaddada cewa, akwai matukar bukatar Nijeriya ta kara kirkiro da sabbin dabarun samarwa da kanta kudaden shiga, musamman domin ta rage wa kanta nauyi.
A cewarsa, basussukan da Nijeriya ke biya daga kudaden shigar da take samu, sun kai yawan kashi 60.
Furceri ya ci gaba da cewa, hakan ya hana gwamnatin kasar, samun damar zuba hannun jari a cikin shirye-shiryenta na inganta rayuwar ‘yan kasar da kuma a fannin tattalin arzikin kasar.
Sai dai, ya yi nuni da cewa, an samu raguwa a kan biyan basussukan da kudin shigar wanda ya ragu daga kash 100, zuwa kashi 60.
Ya bayar da shawarar cewa, kamar kasashe irin Nijeriya, idan har za ta iya habaka kudaden shiggar da take samu, hakan zai bata damar kebe wasu kudaden shigar da kuma ware wadanda, za ta yi amfani da su domin biyan basussukan.
Ya sanar da cewa, yana da kyau Nijeriya ta kara mayar da hankali wajen kara haraji domin ta kara samarwa da kanta kudaden shiga, musamman ta hanyar samar da tsarin bin ka’ida ta yin gaskiya a fannin tara kudin shigar.
Bugu da kari, bisa wani rahoton da sashen sa ido na asusun IMF ya fitar a makon da ya gabata ya yi hasashen cewa, a yanzu Nijeriya matsayin da take biya, ya kai kashi 50.7.
Sai dai, Babban Jami’i ya bayyana cewa, ana sa ran biyan bashin zai ragu da kashi, 49.6 a shekarar 2025.
Rahoton ya bayyana cewa, basussukan sun hada da wasu takardun kudi daga babban bankin Nijeriya CBN da kuma wasu kadarori daga hukumar kula da kadarori ta kasa (AMCN).
Kazalika, rahoton ya sanar da cwa, bisa wani karin hasashen da aka yi ya nuna cewa, bashin zai kara raguwa zuwa kashi 48.5 a 2026, inda kuma zai kara raguwa zuwa kashi 48.2 a 2027.
Har ila yau, rahoton ya ci gaba da cewa, sai dai, za a samu dan karin da zai kashi 48.8 a 2028 da kuma zuwa kashi 49.1 a 2029.
Asusun na ya kuma bayar da shawarci gwamnatin tarayya da ta samar da hanyoyin da za a rage illar hauhawan farashin kaya da kuma kalubalen muhalli da marasa karfi ke fuskanta.