A yayin da wasu daga cikin manoma ke kan girbe amfanin gonar da suka noma a kakar noman bana, wasu barai na kutsawa cikin dare; domin sace wannan amfani da suka noma.
Binciken da wakilinmu ya gudanar a kan wannan al’amari ya tabbatar da cewa, satar amfanin gonar; ya fara ne ‘yan shekarun baya kadan da suka gabata, koda-yake; barayin na fakewa da halin matsin rayuwar da ake ciki ne a halin yanzu.
- CMG Ta Gabatar Da Shirye-Shiryen Talabijin A Peru
- Shugabannin Sin Da UAE Sun Taya Juna Murnar Cika Shekaru 40 Da Kafuwar Huldar Diflomasiyya Tsakaninsu
Kazalika, wadannan barayi na kutsawa cikin gonakin manoman ne tare da sace musu amfanin da suka noma, bayan kammala gibin, ko kafin su kai ga kammala girbin su kwashe amfanin da suka noma.
Wannan dalili ne ya sanya, wasu manoman kan hayi jami’an tsaro na ‘yan sa kai, domin bai wa amfanin nasu kariya daga ire-iren wadanan masu satar amfanin gona.
Hakan ne ya sa wakilinmu ya tattauna da wasu daga cikin wadannan monoma dangane da wannan matsala da ke afkuwa.
LEADERSHIP Hausa, ta kuma ji ta bakin wasu masu fashin baki a kan al’amuran yau da kullum a kan wannan batu.
Haka zalika, wakilin namu ya kuma ji ta bakin wasu Malaman Addinai; a kan hukuncin da littattafan addinan suka tanadar kan masu aikata irin wannan hali na satar amfanin gona.
Daya daga cikin fitattun manoma a Jihar Kaduna kuma Shugabar Gidauniyar Zulifat, a hirarta da LEADERSHIP Hausa ta sanar da cewa, “A halin da ake ciki yanzu, tuni wasu manoman na kan yin girbinsu ne; wasu kuma sun kammala girbin, amma abin takaici shi ne, sai manomi ya gama shan wahala ya kashe kudinsa, yana tunanin dan lokaci kadan amfanin ya rage ya kammala girma, sai barayi su yi masa riga-malam-masallaci; ta hanyar kwashe amfanin da ya noma baki-daya”.
Ta kara da cewa, misali kamar Masara; babu dama manomi ya yi bukka a gonarsa ya zuba ta a ciki, wanda a shekarun baya; ko kadan ba haka abin yake ba, ana iya killace a bukkar a bar ta har zuwa watan sha daya zuwa na sha biyu, ba tare da wata matsala ba, wasu manoman ma a nasu gonakin suke barje ta; su zuba a buhu su kawo gida.
Ta ci gaba da cewa, “Amma yanzu saboda matsala ta satar amfanin, ba mu da halin yin wata bukka a gona; domin kusan akasarin manoman na wasu yankunan, musamman a Arewacin kasar da wannan matsala ta satar ta fi yin kamari, a danyarta muke girbe ta, don gudun ka da aje a sace mata ita”.
“Yanzu, mun zabi mu kwashe ta tana a danyarta mu kawo gida mu shanya ta har ta bushe, maimakon mu bar ta a gona a je a sace ta, wannan abin da barayin ke yi; rashin imani ne, ya kuma kamata su ji tsoron Allah su daina, domin tsadar rayuwa; ba hujja ba ce a kanka ka je ka kwashe amfanin da wani ya jima yana wahala a kai”.
Shi ma wani karamin monomi a Jihar, Malam Adamu Zakari a hirarsa da wakilinmu ya ce, satar amfanin gona ba karamar matsala ba ce, musamman duba da yadda ‘yan bindiga ke sace manoma; domin neman kudin fansa da kuma yadda ‘yan bindigar ke kakaba wa manoma haraji, kafin su bar su su yi noma ko girbe amfanin da suka noma.
“Shin wai da satar amfanin gonar tamu za mu ji, ko kuma kalubalen ‘yan bidndiga, sannan da tsadar kayan aikin gona, musamman takin zamani? Don haka, ya zama wajibi a kan mahukunta, su tanadi dokar da za ta bayar da damar hukunta irin wadannan barayi na amfanin gona”, in ji Zakari.
A bangaren ra’ayin masana a kan wannan batu, fitaccen mai fashin baki a fannin tattalin arziki daga Jihar Kaduna, Dakta Abudllahi Umar Gwandu ya ce, a halin da ake ciki yanzu; musamman a Arewacin Nijeriya, wannan satar amfani abu ne mai muni da ke ciwa manoma tuwo a kwarya.
Ya ce, satar amfanin na gogayya ne da kalubalen rashin tsaron da ake fuskanta, musamman a Arewacin Nijeriya.
Kaza lika ya kara da cewa, matsalar tana kuma yin gogayya da sace moman da ake yi a lokacin da suke kan yin aiki a gonakinsu.
Sai dai, Gwandu ya yi nuni da cewa, satar mutane a guraren ba ta da tasiri ba kamar yadda ake satar amfanin gona ba, wanda kuma abin takaici ne, domin sai bayan manoma sun gama wahala, wasu sun ci bashi daga bankuna; wasu kuma sun sayar da kadarorinsu, sai kawai wasu su biyo dare su kwashe musu amfanin da suka noma, babu shakka; wannan babban abin bakin ciki ne.
A cewarsa, satar na jawo wa manona yin babbar asara matuka, inda ya yi nuni da cewa, abubuwan da suke jawo wa ake yin satar amfanin na da yawa, amma dai muhimmai daga cikinsu guda biyu ne.
Gwandu ya zayyana dalilan kamar haka: Na farko shi ne, talauci da kuma yunwa da wasu mutanen kasar ke fuskanta, wadanda su ne suka yi katutu; ana kuma cikin yanayi mai wahala da tsanani.
Ya kara da cewa, akwai kuma; rashin yin hukunci, satar ma har ta ganganci ake yi; wadda ita ce ma ta fi yawa, domin wata satar ba wai ta yunwa ba ce, don kuwa wasu barayin su kan biyo dare su je gonar manomi da mota su kwashe amfanin da ya noma baki-daya.
Bugu da kari, a bangaren mahangar addinai biyu da muke da su; wato addinin Musulunci da na Kirista, wakilinmu ya ji ta bakin wasu Malamai biyu, musamman dangane da hukuncin da littattafan addinan suka tanadar.
Murshid, daga Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI); reshen Jihar Kaduna, wanda kuma shi ma babban manomi ne; Sheikh Imam Hussani Iliyasu ya ce, satar mafanin da ake yi wa manoma; babban zalunci ne kuma sata ce.
A cewar tasa, Allah bai yarda da zalunci ba; domin kuwa ya haramta zalunci a kansa, ya kuma haramta a kanmu.
“A cikin addinin Musulunci, babu saukale; wato mutum ya zauna ya ki zuwa ya nemi na kansa, saboda haka; ka da Musulmi ya yi amfani da damar kuncin rayuwar da ake ciki a kasar nan, ya je yana satar amfanin gonar da wani manomi ya sha wahala ya kashe kudadensa ya noma, shi kuma barawo ya je ya sace.
“Ina kuma kira ga shugabannin siyasa masu rike da madafun iko, musamman gwamnati, su ji tsoron Allah su tausaya wa al’ummar wannan kasa; wajen sama musu da saukin rayuwa, wanda ta hakan ne za a rage samun irin wadannan barayin da ke satar amfanin da manoman suka noma a gonakinsu”, in ji shi.
Shi kuwa Fasto Yohanna Buru, a zantawarsa da wakilin namu ya bayyana cewa, bisa ga koyarwar addinin Kiristanci; satar amfannin gona, babban zunubi ne.
Ya ce, a cikin litattafi mai tsarki (Bible), Ubanji ya gargadi Kirista ka da ya yi sata a cikin kowane irin hali ya tsinci kansa a ciki na halin rayuwa.
Ya kara da cewa, akwai satar da idan Kirista ya yi; dole a yanke masa hannu, akwai kuma wacce idan ya yi; dole a tausaya masa, domin watakila yunwa ce ta tilasta shi yin satar.
A cewarsa, a cikin littafin karin magana ko kuma a cikin littafin misalai, Ubangiji yana maganar misalai a sura ta shida aya ta talatin; Ubangiji yana magana cewa, idan Kirista ya yi sata a gida ko a gona, saboda yunwa; wannan a tausaya masa a yafe masa ka da a wulakanta shi, amma ba ya yi satar ce don ya yi arziki ba.
Ya kara da cewa, a cikin littafin Lebentika; sura ta goma sha tara aya goma sha daya, duk Kiristan da ya yi sata; ya taka dokar Ubanji ne, kuma akwai hukunci a kan duk Kiristan da ya yi satar ko a ina ne, kuma ko a wanne lokaci; sai dai idan Kiristan na cikin matukar yunwa ne.
A cewar tasa, sata a cikin gona babban laifi ne; sai dai an bai wa mutum dama, idan manomi ya yi girbi; mutum ya je ya yi kalen amfanin gona, ya samu abinda zai ci.