Kungiyar Agajin Munazzamatu Fityanul Islam ta Kasa Reshen Birnin Tarayya Abuja, ta nesanta kanta da wani taro da aka yi na kaddamar da wata sabuwar Kungiyar agaji mai suna “Munazzamatu Fityanul Islam Foundation”.
Wata sanarwa da Kungiyar Agajin Munazzamatu Fityanul Islam reshen Abuja ta fitar Wacce Sakatarenta na Abuja, Salisu Yusuf yasa hannu a madadin Babban Kwamadanta, Abubakar Aliyu Rijana ,ta ce, Wanda ya shirya Wannan Taro, Malam Abubakar S. Yakubu Korarren Tsohon Shugaban Kungiyar ya yi tawaye wa Uwar Kungiyar ta Kasa.
A don Haka sanarwar ta ce wannan sabuwar Kungiyar basa tare da asalin kungiyar ta kasa wacce ke da asali daga Sheikh Mahmud Salga Kano.
Sanarwar ta yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su kwantar da hankalinsu kuma ana nan ana dauka matakan da suka dace a hukumance kamar yadda doka ta tanada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp