Wannan lamarin zai dade yana taimakawa wadanda suka yi ritaya daga aiki ya kasance kuma ba su kai ga daukar mataki ba kan abubuwa ko abinda za su rika yi, bayan sun yi ritaya daga aikin da suka yi a karkashin gwamnati inda suka fi maida hankalinsu kan aiki sosai,amma basu da isasshen lokaci na kansu.
Abinda kowa ya sani ne idan mutum yana aikin da ake ba shi albashi a karshen wata, doka bata ba shi mai aikin ba, damar yin wani abinda zai rika samar ma shi da kudi ba,da zai taimakawa kan shi da iyalansa, babu wani abinda ya zarce aikin noma anan.
- Kakakin Ma’aikatar Tsaron Sin Ya Yi Tir Da Sayar Da Makamai Da Amurka Ke Yi Wa Taiwan
- CMG Ta Gabatar Da Shirye-Shiryen Talabijin A Peru
Ma’aikata lamarin harkokinsu sun dogara ne akan ayyukan da suke yi ana biyansu albashi, kuma yana da matukar wuya su samu lokacinsu, wuraren aikin kadan ne suka bada dama ga ma’aikata su tafi hutu kasar waje,ko kuma su zabi hutun, da kuma wanda ya shafi na lafiya, duk kuma abinda kake son yi sai ka samu izini duk kuma amfanin da zai yi maka a gaba, rayuwa ce wadda bata da wani tasri maikyau, kullum lamarin da akwai takurawa, matsaloli da yawane da suka hada da maganar kudaden mota, abinci, kayan saya, wadanda ba ayi maganarsu ba a cikin albashin da ke badawa.
Yana da matukar wuya ace ga ma’aikacin gwamnati ko hukumar dake zaman kanta a halin da ake ciki yanzu, ya kasance yana ajiye kudi a duk karshen wata bayan an yi albashi, domin kuwa shi lamarin tamkar wani tarko ne aka danawa shi ma’aikacin, kamar ya amsa da hannun dama ne ya bada da hannun hagu,abin ya kasance tamkar wakar da marigayi Fela ya yi, wadda ya sa ma suna “Duk da ana shan wahala akan dan dara” sai dai idan aka fara da wuri a matsayin manomi ko sana’ar noma, kiwon kaji, kiwon dabbobi, ko kuma noman kayan abinci, wani abu kuma shine lamarin lurar ba mai sa damuwa bace da zata damu da kuma amfanar wanda ya yi ritaya daga aiki.
Da akwai bukatar ma’aikata da suke aiki a karkashin gwamnati ko kuma ma’aikatu masu zaman kansu, a rika basu shawara lokacin da suka fara aikin, da ja ma su kunne dangane da yadda za su rika tanadar kudi, su kuma yi nesa da maganar amsar bashi ko sayar da wani abu na su, domin hakan tamkar wata gadar zare ce wadda idan ba sa’a aka yi ba hanya ce da za tayi saurin aika wanda ya amince zuwa kabari cikin sauki,ko karuwar hawan jini, ko farata ga wadanda suka yi ritaya su kan fuskanta.
Wannan lamari ne da ake haduwa da shi a kasashen da suka cigaba amma yafi yawa ga masu tasowa, abin ya zama tamkar wani bala’i ga kasashe da suke ‘yan ya Rabbana ka wadata mu inda masu kudi suke kara kudancewa, kuma matalauta su kra shiga halin fatara, haka gaskiyar take saboda kuwa kudin mutum basu zarce wadanda ya ajiye ko tanada, irin yadda yake ajiye kudi ta haka ne za su taru su yi yawa irin yadda kudi ke shigo maka shi za isa kai da kanka ka gane wurin da ya dace da kai,domin kuwa wurare masu ban sha’awa da burgewa masu kudi ne ko arziki kan zauna a wuraren inda akwai abubuwan more rayuwa, abinda ana yi ma shi wani kallon ko nuna fifiko, saboda abubuwan more rayuwa kamar hanyoyi, Ruwan famfo, wutar lantarki, asibiti, wurin shakatawa, irin hakan wasu ba za su iya samu ba har sai idan ka kasance kana daga cikin ajin wasu za ka iya shiga cikinsu, ko idan kai tsara ba ne babu yadda za ka iya shiga cikin harkar wasu, ko zama kusa da su ko inda suke, har sai idan mutum ya kai bantensa, sai dai kuma rayuwa ita bata san tsara ba sai dai mutum ko mutane.
Wadanda suka yi ritaya da masu amsar fansho da akwai bukatar su rungumi karuwar wasu abubuwa kamar wanda shi yafi dacewa daga cikinsu wato zabin B, manufa dole ne kayi wa iyalanka zabin da zai tsirar daku tare,ya yin da kake aiki inda aka ware ma abubuwan da suka dace kayi da wadanda basu dace ba cikin dokokin,amma kai ma ya dace ka fara tunanin abinda za isa ka tsira lafiya bayan ka yi ritaya.Tunanin da ya dace ka yi ai su iyalanka basu daga cikin sharuddan aikin ka ba kuma tare da su aka dauka ka aiki ba, kamata ya yi ka fara tunanin matakan da suka dace ka dauka tun lokacin da fara aiki ba sai ka, kaiga yin ritaya ba.Ka fara yin wani kasuwanci wanda matarka ko’ya’anka za su lura da shi, sai dai kuma inda ya kasance duk mata da miji suna aiki, sai ayi tunanin da ya dace na abinda za ‘a sa gaba da zai rika samar da kudin shiga,domin babu wani dalilin da za ka bada na zamanka a matalauci ko kai kana baya domin kana da hankalin da za isa kayi tunanin da ya dace.
Ba wani abinda zai sa ka bari a barka a baya ko dai ka yi abinda zai fishsheka ko kuma ka tsaya sai abin ya yi ka, ko dai kana ci gaba ko kuma tafiya irin ta Kura da Hawainiya, cigaba ko shiga cikin rudani irin na masu hakar rijiya, zabi ya rage naka, mutuwa ko rayuwa sai ka zabi daya.
Wadanda suka yi ritaya ba bayi bane amma yadda ake tafiyar da lamarinsu ne ya kai su ga zama bayin, domin akwai tarnaki, da ya hana yin abubuwan da za su bada damar da za ta iya kawo ci gaba, babu wata dama ta tafiya a karo ilimi wanda zai taimakawa wadanda aka yi wa aikin, sai an nemi izini na tafiya karatu, ko hutu, ko hutun shekara, na ‘yan kwanaki, hutun haihuwa, kai nau’oin hutu masu yawa irin dashen da masu mulkin mallaka suka yi, inda shi ma’aikaci wanda shi wurin da yake aikin zai ci gaba amma shi ma’aikacin bai da dama ta ci gaba, babu wani tanadin da aka yi ma wanda zai ma fanshoniya wata rana, maimakon a shigar da abubuwan da za su samar da ci gaban su fanshoniyar da zaman lafiyarsu sai aka bar lamari hakanan kamar miyar da babu gishiri ko magi.
Noma wata sana’a ce ko wani abu da shari’a ta amince da shi domin kuwa bayan da akwai hanya ta sa matarka da ‘ya’ya shiga harkar kasuwanci abinda za ka iya tainakawa sai dai kuma bai da wata alaka shi aikin da ka ke yi, wadannan abubuwa idan an hada su gaba daya ba za su iya canza rayuwar ma’aikaci ba, a kasar saboda babu wani mafi karancin albashin da zai isa ma’aikaci ya tafiyar da rayuwar mafi dacewa, inda rashawa da cin hanci ta lakume lamurra domin tuni akwai tazara main isa da yawa tsakanin masu arziki da Talakawa, idan aka yi la’akari da yadda rayuwa take tafiya musamman a yanzu ba wani abin laifi ba ne idan ma’aikaci yana yin wasu abubuwan da za su rufa mashi asiri da iyalansa, domin kuwa wadanda suka yi dokokin suma basu amfani da su,suna da kamfanoni, hukumomi,da kuma yadda kudade za su rika shigo masu duk sun dauki mataki akan su, amma ma’aikaci wanda yake dama Talaka ne sai yadda suka yi da shi, bama kamar a cikin al’ummar da tsarin tattalin arziki na (Jari Hujja) shi ake ado da shi, ko dai ba komai kasuwa ake sayayya tare, kudade daya kuke amfani da su abu daya shi ne ba za ku je Asibiti daya tare ba, su suna da zabi na iya fita zuwa kasashen waje idan aka yi la’akari da mukamansu.
Da yake an san irin bambancin da ake da shin a yadda rayuwar take da tafiyar da ita, wanda ake biya fanso da wanda ya yi ritaya abu mafi kyau shi ne ya zabi irin rayuwar da zai iya yi, ko dai ya yi rayuwar dai dai wa daida, ko kuma ya kasance abin sai dai hakuri, maganar gaskiya, dan fansho yana iyin duk rayuwar da yaga dama, mafitar ai ba wata mai yawa bace ko? Maganar noma amma ba irin na bayan gida ba wanda ya amsa sunansa, kamar roin na zamani, wato irin noman da zi rika samar da kudaden shiga masu yawa yayin da ake cikin aiki abin yana iya zuwa daga taimakon ma’aikatar gona, domin taimakawa ma’aikatan gwamnati da sayar da kayan da za’a yi amfani da su cikin rahusa, bai kamata a tsaya ma wannan ba domin mutum zai iya farawa da kanshi, da ‘yan kudade ba masu yawa ba, ana iya faraway da kayan noman da suke samr da kudi kamar wake,shinkafa, tumatari, doya karas, masara, gero, citta, kankana, kayan lambu, kiwon kaji, masu kwai da wadanda basu yin kwai, kiwon Awaki,Raguna, Zomo, Dodon- kodi da kuma Aladu,hakananma kiwon Shanu, da sauransu, sai dai abin za ayi amfani da kudi masu yawa, amma idan aka tsara shi kamar yadda ya dace, mai karbar fanshon da wanda ya yi ritaya rayuwa za ta kasance masu mai dadi.