Sama da kilogiram 560,068.31414 na miyagun kwayoyi Hukumar Yaki da Sha da Fatucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA ta kona a ranar Alhamis 4 ga watan Agustan 2022.
Wannan shi ne kaya mafi girma da aka kona a cikin shekaru 32 na tarihin hukumar yaki da muggan kwayoyi.
- NDLEA Ta Kwace Tiramol Miliyan 2.7 A Legas
- NDLEA Ta Damke Wata Mata Za Ta Yi Safarar Miyagun Kwayoyi Zuwa Oman
Manyan jami’an hukumar ta NDLEA, da sauran hukumomin tsaro da sauran jama’a sun halarci taron kona tarin miyagun kwayoyi, inda Shugaban Hukumar, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya ce yin hakan wani sako ne mai karfi ga dillalan miyagun kwayoyi.
Shugaban ya ce za su ci gaba da yin asarar dimbin jarin da miyagu ke kashewa a harkar kwayoyi idan har suka kasa ja da baya da kuma neman wasu halaltattun kasuwanci.
An kona nau’ukan miyagun kwayoyi daban-daban masu nauyin kilogiram 560,068.31414 a wani gajeran taro da aka yi a unguwar Badagary da ke Legas.
Kwayoyin da aka kona sun hada da: hodar Iblis kilogiram 7,414.519; tabar heroin 161,206kg; methamphetamine 1,144.8kg; ephedrine 60,144kg; wiwi mai nauyin 311,416.19162kg ; Khat 10,091.83kg; 273.223kg na tramadol; 0.000170kg na benylin dauke da codeine da 8,207.7505kg na wasu sinadarai masu tayar da hankali.
Reahen rundunar da ke filin jirgin saman Murtala Mohammed (MMIA) da reshen jihar Legas, tare da reshen Seme duk a Legas. An tara kwayoyin ne daga mutanen da babbar kotun tarayya ta samu da laifi kuma ta yanke musu hukunci.