Wata mummunar fashewar Gas ta da ta auku a Magama Jibia, garin da ke kan iyaka a Jihar Katsina, inda mutane da dama suka jikkata, da gidaje da motoci suka lalace.
Fashewar ta faru a wani gidan mai mai suna ‘Walidan’, kuma an danganta lamarin da fataucin gas daga Jamhuriyar Nijar.
- Sojoji Sun Ceto Mata 3, Sun Kwato Makamai A Katsina Da Zamfara
- RaÉ—É—a Ya Kaddamar Da Dakarun Tsaro 550 Kashi Na Biyu A Katsina
Shehu Umar, wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa wata motar dakon silindar gas da aka ajiye tsawon kwanaki a gidan man na iya haddasa fashewar sakamakon wani tartsatsi daga wayar motar.
Wasu da suka gani da ido sun tabbatar da cewa mutane da dama sun sami raunuka, yayin da gidaje, da motoci, da makarantu a kusa da wurin suka lalace. Mazauna yankin sun nuna damuwa kan fataucin gas ba tare da izini ba, suna zargin cewa rashin kulawar hukumomi ya haifar da wannan musifa.
Ana zargin masu fataucin suna cin gajiyar tallafin gas daga Jamhuriyar Nijar, wanda aka yi gwamnatin ƙasar ta yi niyyar yaƙi da hamada.
Mazauna yankin suna kira ga Gwamnatin Nijeriya da ta ɗauki matakan gaggawa don hana irin wannan musifa faruwa a nan gaba, tare da kawo ƙarshen ayyukan fataucin gas a yankin. Yanzu haka dai hukumomi suna kan tantance girman asarar da aka yi, amma har yanzu ba a fitar da wata sanarwa ba.