An ruwaito cewa, kasar Sin ta yi tayin karbar bakuncin taron shugabannin kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta yankin Asiya da tekun Fasifik APEC da za a gudanar a shekarar 2026 inda hakan ya samu goyon baya da kuma amincewar sauran sassan kungiyar a yayin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar na bana.
Da yake tsokaci game da hakan, wani mai magana da yawun Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, Sin ta muhimmanta hadin gwiwar Asiya da yankin tekun Fasifik kuma ta karbi bakuncin taron APEC har sau biyu, daya a shekarar 2001, daya kuma a shekarar 2014. Yanzu, kasar za ta karbi bakuncin taron a shekarar 2026.
Jami’in ya ce, kasar Sin ta shirya tsaf wajen habaka sadarwa da hadin gwiwa da sauran sassan kungiyar game da karbar bakuncin taron na APEC a shekarar 2026 domin a hadu tare a aiwatar da Kudurin Putrajaya nan da shekarar 2024, da zurfafa gina makomar al’ummomin Asiya da yankin tekun Fasifik da samar da yankin ciniki mai ‘yanci da samun kyakkyawan sakamako ta hanyar yin hadin gwiwa a aikace, kana da sanya sabon kuzari ga bunkasa tattalin arzikin Asiya da yankin tekun Fasifik har ma fiye da nan. (Abdulrazaq Yahuza Jere)