Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kone gonakin manoma tare da sace mutane da dama a wasu kauyukan Jihar Zamfara.
Maharan sun fara kai harin ne garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Maru a jihar, inda suka kone gonakin manoma.
- Dan Nijeriya Lookman Na Kan Gaba Wajen Lashe Kyautar Gwarzon Kwallon Kafa Na Afrika Ta Bana
- SSANU Ta Sake Zaɓar Shugaba Wa’adin Shekaru 4
Sun kuma kai wani harin kauyukan Wanke da kuma Zargada inda suka kone amfanin gonar manoma.
Mazauna yankunan da ke iyaka da Jihar Kebbi, sun ce ‘yan bindigar sun sa sun tafka gagarumar asarar amfanin gonar da suka noma, wanda ya hada da masara da auduga, da wake da sauransu.
Maharan sun zo ne gungu-gungu tare da cinna wa gonakin masara da wake da dawa wuta, abin da kuma ya haifar da asara mai tarin yawa.
Sun kuma yi awon gaba da mutane, inda suka kone gonaki da dama, kamar yadda wasu daga cikin manoman da shaida wa manema labarai.
Rahotani na cewa garuruwan Wanke da Zargada da Dan Godabe na daga cikin wadanda maharan suka addaba.