Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yerima, ya ce babu wata yarjejeniya tsakanin jam’iyyar APC da Ahmad Tinubu, na ba shi takarar shugaban kasar nan bayan mulkin shugaba Muhammadu Buhari.
Yerima, wanda kuma dan takarar shugaban kasa ne a jam’iyyar APC mai mulki, ya bayyana hakan a cikin shirin siyasa na Trust Tv, Daily Politics, a daren Juma’a.
- Kwamitin tantance ‘Yan Takarar Shugaban Kasa Na APC Ya Yi Watsi Da ‘Yan Takara 10 Cikin 23
- 2023: Buhari Zai Gana Da Masu Ruwa Da Tsaki Don Fitar Da Magajinsa Gabanin Taron APC
Tinubu, yayin da yake zantawa da wakilan jam’iyyar a jihar Ogun a ranar Alhamis, ya ce lokaci ya yi da zai zama shugaban Nijeriya.
Tsohon gwamnan jihar Legas ya kuma bayyana yadda ya goyi bayan Buhari a takararsa ta shugaban kasa tare da ba da ba Osinbajo mukamin mataimakin shugaban kasa, wanda shi ma a halin yanzu ke zawarcin mukamin shugaban kasa bayan ya gama mataimakin shugaban kasa karo na biyu.
Idan zamu iya tunawa, Jam’iyyar Tinubu, (ACN) ta narke wuri guda da sauran Jam’iyyu a watan Fabrairun 2013, tare da (CPC) da (ANPP) – da kuma wani bangare na (APGA) domin kafa jam’iyyar APC tare da Buhari daga jam’iyyar CPC aka ba shi damar tsayawa takarar babban mukami.
An yi imanin cewa akwai yarjejeniyar da ACN ta yi na cewa za ta fitar da dan takarar shugaban kasa na gaba bayan mulkin Buhari.
Sai dai Yerima ya ce babu wani rahoto da ke nuna an kulla irin wannan yarjejeniya da jam’iyyar.
“Babu wata yarjejeniya da t tabbatar da haka, a lokacin wanene shugaban jam’iyyar? Da farko muna da Cif Bisi Akande, daga baya kuma, muna da John Oyegun, kuma a yau muna da Sanata Abdullahi Adamu, muna da [Mai Mala] Buni a cikin tafiyar da dai sauransu.
“To, ko Cif Bisi Akande ne ya zauna da wasu mutane? Duk wani hukunci da aka dauka a wajen tsarin jam’iyyar ba a amince da shi ba. Jam’iyyar tana da kwamitin ayyuka na kasa, jam’iyyar kuma tana da abin da muke kira NEC kuma akwai bangaren yanke shawara gaba daya wato babban taron kasa.
Ya ci gaba da cewa, “Duk hukuncin da ba a dauka a cikin tsarin jam’iyyar ba, ba hukunci ba ne. Ba za ku iya samun fahimta da mutum ba kuma ku ce ‘hakan zai faru. Idan jam’iyya tana son yanke shawara, ko dai kwamitin ayyuka na kasa ne, ko hukumar zabe ta yanke.
“Idan Yarjejeniyar ta yanke shawara, ba za a iya canza ta ba. Amma za a iya sake duba yanke shawara bisa kowane yanayi. Ko da akwai wannan fahimtar, yanayin yau na iya bambanta da yadda yake lokacin da aka cimma wannan fahimtar. ”
Jam’iyyar APC ta tsayar da ranar 6 ga watan Yuni a matsayin ranar babban taronta a birnin tarayya Abuja, inda za ta zabi dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023.