A safiyar yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dawo Beijing bayan halartar taron shugabannin APEC karo na 31 da taron koli na G20 karo 19, da ziyarar aiki a kasashen Peru da Brazil, wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta yaba a matsayin tafiyar sada zumunci, hadin kai, hadin gwiwa da ba da jagoranci wajen samar da alkibla ga kasashe.
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen ziyarar.
- Jami’i: Kofar Sin A Bude Take Domin Tattaunawa Da Hadin Gwiwa Da Amurka Don Inganta Dangantakar Tattalin Arziki Mai Daidaito
- ’Yan Bindiga Sun Sace ’Yan Uwan Ɗan Jarida a Kogi, Sun Nemi Fansar Naira Miliyan 50
Wang ya ce, a yayin ziyarar ta kwanaki 11 daga ranar 13 zuwa 23 ga watan nan ta Nuwamba, shugaba Xi ya halarci tarurruka kusan 40 na bangarorin biyu da na bangarori daban-daban, ya kuma rattaba hannu kan takardun hadin gwiwa sama da 60, wadanda hakan ba wai kawai ya sa kaimi ga inganta da daidaita ci gaban dangantakar dake tsakanin manyan kasashen ba, har ma ya ba da jagoranci ga kasashe masu tasowa wajen hada kansu da karafawa.
Wang ya kara da cewa, ziyarar ta kara habaka sabbin hanyoyin gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya ga bil Adama, kuma ta samar da sabuwar dama ta diflomasiyya a manyan kasashen duniya mai sigar kasar Sin. (Mohammed Yahaya)