Hauhawar farashin kayayyaki a Burtaniya ya karu a watan da ya gabata saboda karuwar kudin makamashi, kamar yadda alkaluman gwamnati suka nuna.
Hauhawar farashin, ya karu ne da kashi 2.3 a shekarar a watan Oktoba, wanda kari ne daga kashi 1.7 a watan Satumba.
Kudin wutar lantarki da gas da matsakaicin gida ke biya ya tashi ne zuwa £149 a watan da ya gabata, amma dai duk da haka farashin na tashi ne kadan-kadan.
Grant Fitzner, babban masanin tattalin arziki a Hukumar Kididdiga ta kasar ya ce farashin makamashin na cikin abubuwan da suke jawo tashin farashin kayayyaki a kasar.
“Kayayyakin da masana’antu ke bukata sun yi tsada, kuma suna kara tsadar, ga kuma faduwar farashin danyen mai,” in ji shi.
Wani mazaunin Burtaniya mai suna Darren Jones, ya ce gwamnati ta san, “iyalai na shan wahala saboda tsadar rayuwa. Muna tunanin akwai abin da ya kamata gwamnati ta yi.”