Wani yunkurin garkuwa da mutane a karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina, ya kai ga mutuwar wani mutum, sakamakon harbin bindiga.
Lamarin ya faru ne a ranar 24 ga watan Nuwamba, 2024, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai wa motoci biyu hari a kauyen Dan’arau da ke kan titin Magama Jibia, inda suka dinga harbe-harbe.
- Kasar Sin Ta Yi Alkawarin Tabbatar Daidaiton Tsarin Masana’antu Da Na Samar Da Kayayyaki A Duniya
- An Bar Kasashe Masu Tasowa Da Jidalin Sauyin Yanayi
DPO din ‘yansanda na Jibia, ya jagoranci wata tawaga, inda suka fafata da maharan, suka hana su sace mutane, tare da ceto mutane 14.
An garzaya da wasu biyu da suka samu raunukan harbin bindiga zuwa asibiti, amma daya daga cikinsu ya rasu.
Ana ci gaba da kokarin kamo ‘yan bindigar da suka tsere.
Kwamishinan ‘yansandan Katsina, CP Aliyu Musa, ya jinjina wa jarumtakar jami’an tare da kira ga jama’a su rika bayar da bayanai kan duk wani aikin ta’addanci ga rundunar ‘yansanda mafi kusa da su.