Gwamnan Katsina Jihar Katsina, Dikko Radda ya gwangwaje gwarazan Hikayata da kyautar kudade.
Gwamnan ya yi alkawarin bai wa Amra Awwal Mashi kyautar kudi da kuma aikin yi.
- Liverpool Ta Sake Nuna Barakar Real Madrid A Anfield
- Gwamna Yusuf Ya Mika Motocin Bas Na CNG Guda 10 Ga Kungiyar NLC Reshen Kano
Amra wadda ‘yar asalin Jihar Katsina ce, kuma ita ce ta zo matsayi na biyu a gasar Hikayata.
Wakilin gwamnan a wajen taron ne ya bayyana cewa gwamnan ya bai wa Amra kyautar kudi Naira miliyan daya, da kuma daukarta aiki.
Kazalika, ya yi wa mutum 12 da ke kan gaba a gasar kyautar kudi Naira 250,000 kowace.
A ranar Laraba ne BBC Hausa ta yi bikin bayar da kyauta ga wadanda suka yi nasara a gasar rubutu ta Hikayata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp