Majalisar Dattawa ta amince da karatu na biyu na dokokin gyaran haraji guda hudu bayan muhawara a zaman ranar Alhamis.
Shugaban masu rinjaye, Sanata Opeyemi Bamidele ne, ya jagoranci muhawarar, inda yawancin sanatoci suka goyi bayan dokokin, ciki har da Sani Musa, Seriake Dickson, Abba Moro, da Babban Bulaliyar Majalisar, Tahir Monguno.
- ‘Yansanda Sun Kama Barayin Shanu 7 A Jigawa
- Shehu Mahy Inyass Ya Sanar Da Sauye-sauye A Tafiyar Tijjaniya A Nijeriya
Sai dai Sanata Ali Ndume ya yi adawa da dokokin, inda ya cewa ba a yi cikakken shiri game da dokokin harajin ba.
Duk da adawar da ya yi, majalisar ta amince da dokokin ta hanyar kada kuri’a, karkashin jagorancin Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio.
An umarci Kwamitin Kudi na Majalisar Dattawa da ya shirya sauraron ra’ayoyi daga masu ruwa da tsaki tare da gabatar da rahoto cikin makonni shida.