Babbar kotun shari’ar shari’a da ke garin Tsafe, ta jihar Zamfara ta raba wani auren da aka yi tsakanin wani kaka mai suna Musa Tsafe da jikarsa mai suna Wasila Isah Tsafe.
Da yake yanke hukunci, mai shari’a Bashir Mahe ya ce bayan kotu ta saurari bayanin kowane bangare, sai ta gano cewa, auren da suka yi ya saba wa shari’ar Musulinci.
- Jami’an Amurka Na Zuzuta Batun Tarkon Bashi Ne Domin Haddasa Rigima
- Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Sanar Da Matakan Martani Ga Ziyarar Da Pelosi Ta Kai Taiwan
Alkalin ya ce, wannan auren ya saba wa aya ta 73 da ke cikin Suratul Nisa’i, wanda ya zo a shafi na 79 cikin littafin Ashalul Madariki, da shafi na 77 na Ihkamil Ihkami.
Saboda haka sai ya yi bayanin cewa, sakamakon wadannan hujjoji kotu ta raba wannan aure.
Da yake bayani, bayan yanke wannan hukunci, lauyan wanda ake tuhuman Ayuba Abdulahi ya ce, bai yi mamakin yanke wannan hukunci ba,saboda tun da tun da farko bai samu kwarin gwiwar fuskantar wannan kotu.
Majiyar labarin namu ta ci gaba da cewa, Alhaji Musa Tsafe da Hajiya Wasila Isah Tsafe sun dade da yin aure a tsakaninsu har sun haifi yara takwas.
Tun dai a shekara ta 2020 ‘yan uwan ma’auratan suka fara gunaguni cewa wannan auren ya saba wa shari’ar Musulinci.
Saboda haka sai suka kai korafi ofishin Hisbah da keTsafe domin su warware wannan aure, ammam sai ma’auratan suka ce ba su yarda a raba su ba, saboda haka sai hukumar Hisban ta mika wannan koke ga babbar kotun shari’ar Musulinci Shari’a wadda kuma ta yanke hukunci.