Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu kananan yara guda uku a karamar hukumar Ajaokuta da ke jihar Kogi, kuma suna neman kudin fansa N100m.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Ayah, ya tabbatar da sace mutanen a ranar Juma’a.
- Tuwon Amala Ya Yi Sanadin Mutuwar Mutum Biyar A Kogi
- Da Dumi-Dumi: Wani Abu Ya Fashe A Ofishin Gwamnatin Kogi
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce kwamishinan ‘Yansandan jihar, Edward Ebuka, ya tura jami’an ‘Yansanda da ke sassa daban-daban na yaki da garkuwa da mutane tare da hadin guiwar ‘yan banga da mafarauta domin bin diddigin masu garkuwa da mutane domin kubutar da yaran.
An yi garkuwa da yaran uku masu shekaru uku da biyar da shekaru goma a yammacin Larabar da ta gabata da misalin karfe takwas na dare a gidansu da ke Kaduna Estate, Ajaokuta Steel Township.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen da ke dauke da bindigogi sun yi ta harbe-harbe ba dadewa, inda suka tsorata mazauna yankin kafin su yi awon gaba da yaran.
Wani dan uwa da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun tuntubi ‘yan uwa inda suka bukaci a biya su N100m. Lamarin ya zo ne kwanaki kadan bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘Yansanda uku da ‘yan banga biyar a Jida-Bassa a karamar hukumar Ajaokuta ta jihar.
A wani mataki na dakile kalubalen tsaro da ake fama da shi a jihar Kogi, gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya bayar da umarnin rufe dukkanin gidajen karuwai tare da haramta amfani da abin rufe fuska a wuraren taruwar jama’a domin tantancewa.