Ana bukatar manomi ya tabbatar ya gyra gonarsa kafin ya shuka shi, sannan ya yi wa gonar haro yadda amfanin zai kama kasar noman sosai, kazalika ana so manomi ya yi amfani da gonar da ta shafe shekaru biyu ba a yi noma a cikinta ba, musaman don kare amfanin daga kamuwa da cututtuka.
Lokacin Yin Shuka:
An fi so a yi shuka a farkon kakar damina, misali daga watan Maris zuwa na Afirilu; ana kuma so a gyara Irin nasa ta hanyar yanka shi zuwa kanana daga kimanin mita 30 zuwa mita 35 ko kuma daga mita 35 zuwa mita 40.
- Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (2)
- Sharhin Littafin Zube Na ‘Sidi Ya Shiga Makaranta’ Na Umaru Ladan Da Michael Crowder (4)
Idan kuma Irin ya yi kankanta sosai, manomi ba zai samu amfani mai yawa ba, kazalika Dankalin Turawan da aka shuka kuma; na fara ruba ne bayan sati biyu.
Zuba Masa Takin Gargajiya:
Ana so manomi bayan sati biyu da shuka shi, ya zuba masa takin gargajiya.
Yi Masa Noma:
Bayan manomi ya shuka shi da ‘yan kwanaki, ana bukatar ya yi masa noma bayan ya shuka shi.
Kare Shi Daga Kamuwa Da Cututtuka:
Ana bukatar manomi ya tabbatar yana sa ido sosai, don kare shi daga kamuwa da cututtuka.
Lokacin Girbi:
Idan manomi ya shuka shi ne a watan Afirilu, zai iya girbe shi a watan Agusta, domin yana nuna ne gaba-daya bayan kwana dari, amma ya danganta da irin nau’insa da aka shuka; sannan kuma, ana gane ya nuna ne bayan ganyensa ya koma yalo.
Har ila yau, ana so a bar shi a cikin kasar nomansa har zuwa daga sati biyu zuwa uku kafin a girbe shi.
Adana Shi Bayan An Girbe Shi:
Ba a so manomi ya wanke shi kafin ya adana shi, domin kuwa hakan zai iya jawo a rasa ingancinsa da kuma dandanonsa.
Ana so manomi ya adana shi busasshen waje, har zuwa sati biyu kafin ya adana shi, an kuma fi so a adana shi a wajen ajiyar da ke da ma’aunin yanayin da ya kai 30.
Sayar Da Shi:
Manomi na iya kai shi manyan shaguna, manya-manyan otel ko kuma kasuwa; don sayar da shi.