Wani rahoto da wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa Ekuality Now ta fitar, ya ce ma’anar fyade a kasashen Afirka 25 ya ba da dama ga masu aikata laifuka su tafiyarsu ba tare da an tuhume su da wani laifi ba.
Sakamakon binciken wani bangare ne na wani bincike mai shafuka 46 da ya bankado gibi a fannin dokoki da aiwatarwa da kuma samun adalci ga wadanda aka yi wa fyade a kasashen Afirka 47.
- An Yi Wa Matashi Hukuncin Daurin Rai Da Rai Kan Yi Wa Yarinya Fyade A Kebbi
- Yara Mata Miliyan 370 Ke Fuskantar Cin Zarafi Da Fyade A Duniya –UNICEF
Rahoton ya ce a duniya kashi 35 cikin 100 na mata sun fuskanci cin zarafi na jiki ko na lalata, kuma kusan kashi 33 cikin 100 na mata a Afirka sun fuskanci cin zarafi a rayuwarsu.
Rahoton ya ce an samu karuwar yawan cin zarafin mata a lokacin tashe-tashen hankula a kasashen Habasha da Sudan da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, in ji rahoton, wanda ya kara da cewa a wadannan kasashe, ana amfani da fade a matsayin makamin yaki wajen bata wa al’umma rai.
Sally Ncube, wakiliyar yanki ce ta Ekuality Now a kudancin Afirka a Yanzu.
Ta fadawa Muryar Amurka ta wata manhajar aika sako daga kasar Zimbabwe cewa takaitattun ma’anar fyade da aka dade suna karfafa rashin hukunta masu aikata laifuka a kasashe da dama.
Ta ce “Misali, fyade da aka aikata a cikin kusanci da abokin tarayya, ana mayar da wadannan laifuka zuwa kananan laifuka, tare da kananan hukunce-hukunce da ke haifar da wani sako mai rudani game da cikakken hakkin kowane mutum na cin gashin kansa.”
Rahoton ya bayyana sunayen kasashe 25 na Afirka, inda ma’anar fyade da doka ta tanada ya yi kadan. Sun hada da Kamaru da Sudan ta Kudu da Chadi da Ekuatorial Guinea da Gabon da Gambia da Mozambikue da kuma Malawi.
Zione Lapani ita ce mai daidaita sashin tallafawa wadanda abin ya shafa a ofishin ‘yan sanda na Blantyre a Malawi.
Ta fadawa Muryar Amurka wani lamari da wata matar aure ta kai karar ‘yan sanda bayan da mijin ya yi lalata da ita.
Lapani ta ce ba su bude wata kara ba bayan tattaunawa da ma’auratan da suka tabbatar da cewa, mutumin ya tilasta wa matarsa yin lalata da ita na tsawon lokaci saboda wasu batutuwan iyali.
Wani rahoto na Ekuality Now game da gibi a cikin dokokin iyali da aka fitar a farkon wannan shekarar, ya gano cewa dokar al’ada ta Malawi tana daukar amincewar har abada don yin jima’i a cikin aure, kuma mace za ta iya hana mijinta yin jima’i ne kawai idan ba ta da lafiya ko kuma ta hanyar rabuwa bisa doka.
Sai dai kuma rahoton ya ce kasar Rwanda ta dauki muhimman matakai domin inganta binciken wadanda zalunta, tare a hukunta laifukan cin zarafin mata.
Har ila yau, ta ce Senegal ta dauki irin wannan matakin ta hanyar kafa “Cibiyoyin doka” da ke ba da taimakon shari’a da zamantakewa.
Kuma a Malawi kotuna sun fara yanke hukunci mai tsauri ga wadanda aka samu da laifin fyade.
Misali, a shekara ta 2021, wata babbar kotu a kudancin Malawi ta yanke wa wani mutum dan shekara 33 hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari, saboda ya yi wa yarinya ‘yar shekara tara fyade.