Jaridar Leadership ta zaɓi Bambo Akani a matsayin gwazon shekara ta 2024 a fagen wasannin motsa jiki, kan ƙwazonsa na ƙarfafa guiwa da burinsa na sanya Nijeriya ta zama sahun gaba-gaba a fagen wasannin motsa jiki, da kuma samarwa matasa masu tasowa kyakkyawar makoma a fagen wasanni. Bambo Akani, wanda ya kafa kungiyar “Making of Champions Ltd (MOC)”.
Jagorancin Bambo Akani, hangen nesansa ya samar da shirin samar da gwarazan ‘yan wasa (MOC), samar da kafar watsa labarai a ɓangaren wasanni don ɗaukaka martaba da shirye-shiryen wasanni a Nijeriya, da sauran ƙasashen nahiyar Afirka, kuma ya himmatu wajen ganin ci gaban da wasanni za su kawo a Nijeriya da Afirka baki ɗaya.
- ‘Yansanda 4,449 Sun Kai Karar Babban Sufeta Na Kasa Bisa Jinkirin Karin Girma
- Jerin ‘Yan Wasa Uku Da Suka Zura Kwallaye 100 A Gasar Zakarun Turai
Shirinsa na samar da gwarazan ‘yan wasa, ya fara ne a shekarar 2013, tare da samar da wani taƙaitaccen tarihin wasannin motsa jiki na (Olympics) da Nijeriya ta taka a baya, kasancewar Nijeriya ƙasa ce mai albarka ɗauke da mutane masu yawa a fagen wasannin motsa jiki.
Bambo Akani, ya yi imanin cewa, Nijeriya na da ƙarfin da za ta iya ƙalubalantar ƙasashe irin su Amurka da Jamaica a fagen wasannin motsa jiki, saboda akwai masu ɗimbin basira da za su sa ƙasar ta zama jigo a fagen wasanni. Yana mai cewa, “ya kamata Nijeriya ta kere Jamaica da Amurka idan har ‘yan wasan sun sa himma da gaske wajen ganin hakan ta tabbata”.
Don haka, bayan shekaru da dama ana ƙoƙarin ganin an dawo da martabar Nijeriya a fagen wasannin motsa jiki, tare da zurfin sanin Bambo Akani a fagen wasannin Olympics, a matsayinsa na haziƙin marubucin wasanni, mai daukar hoto da sanin makamar aiki, MTN ta ɗauki nauyin wani shirin wasannin a ƙarƙashin makarantar wasanni ta MOC a shekarar da ta gabata ta 2023.
Shirin na da manufar lalubo hanyoyin haɓaka haziƙan masu wasannin motsa jiki a ko’ina a duk faɗin Nijeriya, an bude makaranta wacce aka yi wa laƙabi da ‘Jamaican High School CHAMPS’. A cikin watan Agustan bana, an kaddamar da ajin farko na ‘yan wasa 20 na kakar wasa ta biyu na MTN CHAMPS a makarantar horas da wasannin motsa jiki ta MOC da ke Legas.
’Yan wasan da suka haɗa da maza bakwai (sprinters) da maza biyar (quarter milers) da mata biyar (sprinters) da kuma mata uku (quartermilers), an zaɓo su ne daga cikin ’yan wasan da suka yi fice a kakar wasa ta biyu na farkon gasar MTN CHAMPS da MOC ta gabatar a jihohin Akwa Ibom da Abia da Anambra da Filato da Kano da Neja da Osun da Oyo da kuma Jihar Ribas.
Matasa da dama, sun dauki wasanni a matsayin nishaɗi na ɗan wucin gadi, amma ga waɗannan gwarazan ‘yan wasa matasa 20, hanya ce ta samun kyakkyawar makoma, wannan babbar jinjina ce ga shirin MOC.
A wani ɓangare na hadin guiwar da MTN ke yi da MOC, ‘yan wasa 20 ɗinnan, za su samu damar amfani da kayayyakin motsa jiki kyauta da samun malamin horo kwararre da kuma tsarin ci gaba da samun kyakkyawar kulawa mai inganci na tsawon zamansu shekara guda a makarantar, wanda aka tsara shi don bunƙasa ƙwarewarsu don su shiga a dama da su a gasar ƙasa da ƙasa, kamar wasannin gamayyar ƙasashe rainon Birtaniya (Commonwealth) da na Olympics.
Saboda samun irin waɗannan yunƙuri wanda ba a taɓa ganin irinsa ba a Nijeriya, hakan ya sa ta zama ƙasa ɗaya daga cikin manyan ƙasashe da ke samun lambar yabo a wasannin motsa jiki ta duniya, don haka Bambo Akani ya cancanci wannan lambar yabo.