• English
  • Business News
Monday, October 27, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ɗangote Ne Gwarzon Jaridar LEADERSHIP Na Shekara Ta 2024

by Leadership Hausa
11 months ago
dangote

Alhaji Aliko Dangote, wanda aka fi sani da babban ɗan kasuwa kuma wanda ya fi kowa arziki a Afrika, ya zama wata alama da ke nuna ci gaba da bunƙasar tattalin arziƙi a nahiyar.

Dangote ya kasance ginshiƙi wajen kawo sauye-sauye a fannin masana’antu da rage dogaro da shigo da kayayyaki, a ƙoƙarinsan na tabbatar da wadatar kayan masarufi a cikin gida. Wannan karramawa ta Gwarzon Shekara ta 2024 ta tabbatar da irin tasirinsa a harkar masana’antu, da ci gaban al’umma, da kyautata rayuwar jama’a a duk faɗin Afrika.

  • Dangote Ya Rage Wa ‘Yan Kasuwa Farashin Man Fetur
  • Matatar Dangote Ta Fara Fitar Man Fetur Dinta Zuwa Kasashen Afrika

Tarihi da Farko na Rayuwa

An haifi Aliko Dangote a Kano, Nijeriya, cikin iyali masu rikon gaskiya da goge wa a kasuwanci. Kakansa, Alhaji Sanusi Dantata, ya kasance ɗaya daga cikin manyan attajirai a Afrika ta Yamma, wanda ya kafa babban kamfani na cinikin gyada. Wannan tarihi na kasuwanci ya tasirantu ga Dangote tun yana ƙarami, inda ya nuna sha’awar shiga kasuwanci tun yana makarantar firamare.

Karatu da fara Kasuwancinsa

LABARAI MASU NASABA

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Dangote ya yi karatu a Jami’ar Al-Azhar, Cairo, ƙasar Masar, inda ya samu digiri a fannin kasuwanci. Bayan dawowa Nijeriya a 1978, ya samu bashin Naira 500,000 daga ƙanin mahaifinsa, Alhaji Sanusi Dantata. Wannan rance ya ba shi damar fara kasuwancin kayayyaki kamar siminti, da shinkafa, da sukari, da shinkafa, tare da mayar da hankali kan buƙatun jama’a da kuma rage giɓin kayan masarufi a cikin gida.

A yayin gudanar da kasuwancin sayar da kayan masarufi, Dangote ya fahimci cewa dogaro da shigo da kaya daga ƙasashen waje na kawo cikas ga haɓakar tattalin arziki. Ya yi tambayoyi masu muhimmanci kamar: “Me ya sa za a ke shigo da sukari idan za a iya samar da shi cikin gida?” Wannan tunanin ya sa ya koma masana’antu, inda ya kafa kamfanoni da suka shafi sukari, da gishiri, da siminti. Wannan mataki ya zama ginshiƙin arziƙinsa kuma ya sauya za yanayin masana’antu a Nijeriya da Afirka baki ɗaya.

Masana’antu

Kamfanin Simintin Dangote ya zama babbar masana’antar siminti a Afrika, yana samar da kayan gini da suka rage dogaro da shigo da kaya. Wannan nasarar ta tabbatar da matsayin Dangote a matsayin jagora a harkar masana’antu. Bugu da ƙari, ya ƙaddamar da shirin samar da sukari da man fetur, wanda ya ƙara wa tattalin arzikin Nijeri ya ƙarfin gwiwa.

Matatar Dangote

Matatar Dangote, wadda ke Legas, ta zama babban ginshiƙi a harkar makamashi a Afirka. Wannan masana’anta mai iya sarrafa ganga 650,000 na mai a kowace rana, tana rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje. An kaddamar da masana’antar a watan Mayu na 2023, kuma ta fara samar da dizal da man jirgin sama a farkon 2024.

Haka kuma, wannan masana’antar ta fara samar da Fetur (Premium Motor Spirit (PMS) a watan Satumba 2024, wanda ya kawo sauyi mai girma wajen rage shigo da man fetur. Matatar Dangote ta taimaka wajen rage asarar kuɗaɗe ta hanyar kawar da buƙatar shigo da man fetur daga ƙasashen waje, tana ceton Nijeriya kimanin dala biliyan 7.32 a duk shekara.

 

Gudummawar A Fannin Tattalin Arziki Da Samar Da Aiyuka

Dangote ya zuba jarin sama da dala biliyan 25 a fannonin masana’antu, wanda ya haifar da damar samun aiki ga miliyoyin mutane. Masana’antu kamar kamfanin Simintin Dangote, da na Sukari Dangote, da Matatar Dangote sun kasance ginshiƙi wajen rage rashin aikin yi da kuma haɓaka tattalin arziki a Nijeriya da sauran ƙasashen Afirka.

 

Kyautata Rayuwa

Ta hanyar Gidauniyar Aliko Dangote Foundation (ADF), Dangote ya ba da tallafi ga fannonin kiwon lafiya, da ilimi, da rage talauci. An kafa wannan gidauniya a 1994, sannan aka sake mata suna zuwa Aliko Dangote Foundation a 2018. Gidauniyar ta fi mayar da hankali kan magance rashin abinci mai gina jiki, yaki da cututtuka kamar na annobar irinsu polio, da Ebola, da COVID-19, da kuma bayar da tallafi ga waɗanda bala’o’i suka shafa kamar ambaliya.

 

Nasara da Lambar Yabo

A 2008, Dangote ya fara bayyana a jerin masu arziƙi na mujallar Forbes, kuma tun daga nan ya kasance mai tasiri a duniya. A 2011, ya zama mutum na farko a jerin attajirai 40 na Afrika. Haka kuma, ya sami lambobin yabo daban-daban, ciki har da GCON daga gwamnatin Nijeriya a 2011, Grand Commander of the National Order of the Republic of Benin (2013), da Commander of the National Order of Valour na Kamaru (2021).

 

Jagoranci a Kasuwanci

A matsayin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya tabbatar da cewa jagoranci na gaskiya da hangen nesa zai iya kawo ci gaba mai ɗorewa. Rukunin kamfanonin Dangote na aiki a ƙasashe 17 na Afrika, hakan yana tabbatar da cewa yana taimakawa wajen bunƙasa masana’antu da tattalin arziƙin nahiyar baki ɗaya.

 

Halayen Jagoranci Da Mutunci

An san Dangote da sauƙin kai, da riƙon amana, da jajircewa wajen ganin Afrika ta zama mai dogaro da kai. Salon jagorancinsa ya sa kamfanoninsa suka zama abin koyi a duniya.

 

Tasiri Mai Dorewa

A yau, Dangote ya kafa tarihi a harkar masana’antu da tattalin arziƙi. Ya zama gwarzon da ya bunƙasa masana’antu a Afrika, ya mai da hankali kan rage talauci da kuma haɓaka rayuwar jama’a. Wannan lambar yabo ta Gwarzon Shekara ta 2024 ta tabbatar da irin rawar da ya taka wajen sauya yanayin tattalin arziƙin Afrika, tare da zama abin koyi ga shugabanni da ƴan kasuwa masu tasowa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

dangote
Labarai

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa
Labarai

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Next Post
Amfanin Atisaye Ga Mai Juna-biyu

Amfanin Atisaye Ga Mai Juna-biyu

LABARAI MASU NASABA

dangote

Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa

October 27, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno

October 27, 2025
Hatsarin Jiragen Ruwa

Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe

October 27, 2025
Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

Tunawa Da Dawowar Taiwan Kasar Sin Shekaru 80 Da Suka Wuce Yana Da Ma’ana Sosai

October 26, 2025
Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga Miliyan 1.4 Kullum

October 26, 2025
Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya

October 26, 2025
“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

“Ba Gudu Ba Ja Da Baya Game Da Tsarin “Call-up system” A NPA”

October 26, 2025
Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

Ya Zuwa Satumban Bana Adadin Lantarki Da Sin Ta Samar Ya Karu Da Kaso 17.5%

October 26, 2025
Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

Dalilin Da Suka Sa Hisbah Ta Dakatar Da Auren Ƴan TikTok A Kano

October 26, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Gwarzon Ma’aikacin Gwamnati Na Shekarar 2025, Dakta Zacch Adedeji

October 26, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.