Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu lambar yabo ta Gwarzon Gwamnan Shekara ta 2024 ta Jaridar Leadership, saboda gagarumin aikin da ya yi a fannin ilimi da sauran muhimman ɓangarorin ci gaba a Jihar Kano.
Gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ilimi tare da ware kashi 31 na kasafin kuɗin jihar na Naira biliyan 570, kwatankwacin Naira biliyan 165.4, a ɓangaren ilimi. Wannan matakin na nufin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, wadda Kano ce ke kan gaba na mafi yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya, da kuma bai wa yara marasa galihu damar samun ingantaccen ilimi.
- Gwamna Yusuf Ya Mika Motocin Bas Na CNG Guda 10 Ga Kungiyar NLC Reshen Kano
- Kano Ta Kaddamar Da Cibiyar Tafi-da-gidanka Ta Farko A Nijeriya Don Yi Wa Motoci Lasisi
Gwamna Yusuf ya yi sabbin gine-gine a makarantu, ya samar da kujeru da tebura da sauran kayan karatu. Haka kuma, gwamnatinsa ta bayar da tallafin karatu ga matasa maza da mata da yawa don yin karatu a ƙasashen waje, don tabbatar da cewa ilimi ya zama ginshiƙin ci gaban jihar.
Shahararsa da kalaman “ilimi, ilimi, ilimi” sun tabbatar da cewa ɓangaren ilimi shi ne abin da ya fi bai wa fifiko.
An haifi Alhaji Abba Kabir Yusuf a gidan Sarautar Fulanin Sulluɓawa, wanda suke wani tsagi ne daga sarakunan Masarautar Kano. Ya yi ƙuruciyarsa a Gaya, a hannun kakansa, Alhaji Yusuf Bashari, Hakimin Gaya. Ya yi karatunsa na Firamare da Sakandire a Kano kafin samun difiloma a Fannin Injiniyan Ruwa da Muhalli a Kwalejin Fasaha ta Mubi da Kaduna Polytechnic.
Daga baya, Gwamna Yusuf ya samu shaidar digiri a fannin gudanarwa a Jami’ar Bayero ta Kano. Abba Kabir Yusuf ya fara aikinsa a Hukumar Ruwa ta Jihar Kano, inda ya samu gogewa a fannin aikin gwamnati. Har ila yau, ya taɓa riƙe muƙamin shugaban kwamitin gudanarwa na Cibiyar Shirye-shiryen Ilimi da Gudanarwa ta Ƙasa.
A siyasance, Abba Kabir Yusuf ya fara aikinsa a ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, inda ya riƙe muƙamai daban-daban, ciki har da mataimaki na musamman da muƙamin sakatare na musamman da muƙamin babban sakatare, da kuma Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na Jihar Kano.
A shekarar 2018, ya tsaya takarar gwamna ƙarƙashin jam’iyyar PDP, wanda daga nan ne ma ya samo laƙabin sunan “Abba Gida-gida.” Duk da cewa bai yi nasara ba a wancan lokacin, amma bai karaya ba. A shekarar 2023, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP tare da Jagoransa Sanata Kwankwaso, kuma ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Bayan lashe zaɓen, Abba Kabir Yusuf ya fuskanci ƙalubale na siyasa, ciki har da soke zaɓensa a kotun sauraron ƙararrakin zaɓe. Sai dai, ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun Ƙoli, inda aka tabbatar da zaɓensa a matsayin gwamnan jihar a watan Janairu 2024. Wannan ƙarfin hali da juriya da ya nuna sun ƙara masa daraja a matsayin shugaba wanda ba ya barin wani abu ya shagaltar da shi daga ƙoƙarin ciyar da jiharsa ta Kano gaba.
A wajen inganta rayuwar al’ummar Kano kuwa, Gwamna Yusuf yana gina sabbin gadoji a Ƙofar Dan Agundi da Tal’udu, domin rage cinkoson ababen hawa a jihar. Haka kuma, ya inganta fannin kiwon lafiya ta hanyar samar da kayan aiki da magunguna a asibitoci kyauta. Gwamnatinsa ta kuma ƙaddamar da shirin tallafa wa mata 5,200 da kuɗi Naira 50,000 a matsayin jari. Wannan tallafi na nufin taimaka wa mata wajen ƙarfafa wa kasuwancinsu da rage talauci a tsakaninsu.
Haka kuma, gwamnatinsa ta canza fitilun kan titunan Kano zuwa masu amfani da hasken rana, wanda ya sanya titunan jihar zama cikin haske ko yaushe tare da rage amfani da makamashi mara tsafta. Gwamna Yusuf yana biyan albashi, fansho, da kuɗin sallama akai-akai, kuma ya kasance cikin gwamnonin farko a Nijeriya da suka fara aiwatarwa da biyan mafi ƙarancin albashi na Naira 71,000. Bugu da ƙari, gwamnatinsa ta biya bashin Naira biliyan 3.5 na ƙasashen waje da Naira biliyan 60 na cikin gida, ta rage bashin jihar zuwa Naira biliyan 127.8 a tsakiyar shekarar 2024.
Alhaji Abba Kabir Yusuf ya zama jajirtaccen gwamna wanda ya yi fice wajen kawo sauyi a fannin ilimi da lafiya da gine-gine da kuma tallafa wa jama’a. Jagorancinsa ya zama abin misali a Nijeriya, burinsa bai wuce sanya murmushi a fuskar Kanawa ba.