Ministan Muhalli a Nijeriya, Alhaji Balarabe Abbas Lawal ne ya yi nasarar zama gwarzon shekara ta 2024 na Jaridar Leadership, saboda hangen nesansa da kyawawan manufofinsa da ya aiwatar a ma’aikatarsa ta muhalli, wanda ya yi tasiri da kawo sauyi a É“angaren kula da muhalli a Nijeriya a Æ™arÆ™ashin gwamnatin shugaban Æ™asa Bola Ahmed Tinubu.
Samar da Kyakkyawan tsari da zuwa da sababbin sauye-sauye waje kula da muhalli, ya bayar da gudummawa sosai kan tsaron kasa da samar da bunƙasar tattalin arziƙin ƙasa, ya sa Balarabe Lawal ya zama fitila a tsakanin takwarorinsa ministoci.
- Gwamnan Sakkwato Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2025 Na Biliyan 526
- Gwamna Radda Ya Kaddamar Da Shirin Ci Gaban Al’umma
Manyan nasarorin da Lawal ya samu sun biyo bayan sabon tsarinsa na yaki da sauyin yanayi da farfaɗo da muhalli a Nijeriya. A Jagorancinsa ya ƙaddamar da wasu tsare-tsare da za su magance matsalolin da suka daɗe ana fama da su a Nijeriya, tare da aiwatar da sababbi da ya da za su magance barazana ga muhalli.
Nasarar da aka samu ta tsaftace Ogoni, lamarin da ya Æ™i ci- ya Æ™i cinyewa, amma a Æ™arÆ™ashin jagorancin Lawal an ga Æ™arshensa, ya samu yabo iri-iri daga al’umma daban-daban a ciki da wajen Æ™asa kan wannan gagarumin aiki.
Lawal ya samu yabo da goyon bayan al’umma, ta hanyar samun hadin kan masu ruwa da tsaki daga cikin shugabannin yayin kaddamar da ayyukan ma’aikatarsa, kamar tsarin samar da tsaftataccen ruwa a Æ™arÆ™ashin Cibiyar Inganta Muhalli a Wiiyakara. Wannan shaida ce ga sadaukarwarsa don farfaÉ—o da cibiyoyin inganta muhalli da jin daÉ—in al’umma.
Saurin fahimtar matsalar sare Bishiyoyi, Lawal ya jagoranci rarraba irin Bishiyoyi miliyan 45 a faɗin ƙasa baki ɗaya. Wannan gagarumin ƙoƙarin yaƙi da sare Bishiyoyi, da kuma sake shuka wasu a gandun daji ya taimaka wajen yaƙi da kwararowar hamada da inganta yanayin muhalli.
Shirin ‘Agro-Climatic Resilience in SemiArid Landscapes (ACReSAL),’ shirin ya dawo da darajar kadada 350,000 da ta gurbace. Wannan yunÆ™urin na nuna kishin al’umma da Æ™asa da ake fama da kwararowar hamada da sauyin yanayi.
Fahimtar muhimmancin tattalin arzikin Nijeriya a tafkin Chadi, Lawal ya jagoranci yunkurin ƙasa da ƙasa na dawo da darajar yanayin tafkin. Haɗin guiwa tare da abokan hulɗa na duniya daga EU da UAE da Kanada, ya samar da nasarori masu muhimmanci da suka haɗa da dabarar datsewa da sauyawa ruwa hanya, da kuma samar masa da yanayin kula mai dorewa. Lallai wannan shugaba yana da zimma da ruhin aiki da kuma kishin ganin ingantaccen yanayi mai dorewa a Nijeriya.
Saboda sadaukarwarsa da kula da muhalli, ya tabbatarwa duniya cewa jagoranci nagari zai haifar da sakamako na ban mamaki. Don kishin ƙasa da jagoranci nagari wajen gina ƙasa da ci gabanta mai dorewa, Balarabe Abbas Lawal shi ya lashe kyautar LEADERSHIP na Gwarzon Jagoran Kula da Muhalli na Shekarar 2024.
Lawal ya sanya Nijeriya a babban matsayi mai daraja a ƙasashen duniya kan shirin kula da yanayi da muhalli a ƙawancen duniya (COP28).