Wasu jiga-jigan masu fada a ji a yankin arewa sun shiga tsakani don warware rikicin siyasar da kunno kai bayan dakatarwar da shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar Arewa ‘Consultatibe Forum’ (ACF), Mista Mamman Mike Osuman.
Mataimakin Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT), Ambasada Ibrahim Maisule ne ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta musamman a Abuja.
- Ali Nuhu Ya Zama Jakadan Kamfanin Tsaftace Haƙora A Arewacin Nijeriya
- Hukumar NDLEA Ta Kama Mutane 14,480 A Cikin Watanni 10 – Marwa
A karshen makon da ya gabata ne dai aka dakatar da shugaban kwamitin zartarwa na kungiyar ACF bisa wasu kalamai da ya yi da suka shafi siyasa, wadanda kwamitin amintattu da wasu mambobin kungiyar suka yi watsi da su.
A cikin wata wasika tare da sa hannun babban sakataren kungiyar ACF, Malam Murtala Aliyu da shugabannin BoT, Alhaji Bashir Dalhatu, Mista Osuman, an zargi Mista Osuman da yin kalamai marasa izini da ke nuna cewa arewa za ta mara wa dan takarar shugaban kasa daga arewa baya a 2027.
Wasikar ta ci gaba da cewa, “An jawo hankalin kungiyar kan wasu bayanai da aka rika yadawa ga Mista Mamman Mike Osuman, SAN, OFR, Shugaban kwamitin zartarwa na ACF na kasa, wadanda aka yi a yayin taron kungiyar wanda aka yi a ranar Laraba, 20 ga Nuwamba, 2024, a hedkwatar ACF da ke Kaduna.
“An ji Mista Osuman yana cewa arewa za ta mara wa dan takarar shugaban kasa daga arewa baya a 2027. Shugaban kungiyar ya yi wadannan kalamai ne ba tare da tuntuba ko tattaunawa da wasu shugabanni da mambobin kungiyar ta ACF ba, don haka ya nuna ra’ayinsa ne kwai.
“ACF ta yi watsi da kalaman Mista Mamman Mike Osuman gaba daya. Don haka ne shugabannin kwamitin amintattu na ACF (BOT) da na gudanarwa ta NEC suka yanke shawarar dakatar da Mista Mamman Mike Osuman nan take.”
Sai dai Mista Osuman, ya yi zargin cewa ba a yi masa adalci ba wajen tsarin da aka bi na dakatar da shi.
An dai bayyana cewa, Mista Osuman ya tara tawagar manyan lauyoyin ne tun a karshen makon da ya gabata, a shirye-shiryen shigar da karar na kalubalantar dakatar da shi daga mukaminsa.
Wasu majiyoyi na kusa da shi sun ce ya tattara manyan lauyoyin Nijeriya guda takwas masu mukamin SANs da nufin kalubalantar dakatar da shi a kotu.
Bugu da kari, wasu majiyoyi na kusa da BoT da kuma NEC na kungiyar sun shaida cewa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Alhaji Mahmud Yayale Ahmed ya kira taron masu ruwa da tsaki a ranar Talata a Abuja, inda suka tattauna kan bukatar gaggawa don magance rikicin wajen guje jefa ACF cikin wani babban rikicin siyasa.
An tattaro cewa, za a ci gaba da taron ne a ranar Asabar, yayin da karin shugabanni a yankin arewa ke kokarin ganin an shawo kan rikicin cikin gaggawa.
Ambasada Maisule ya bayyana kwarin gwiwa game da shirin sulhun, inda ya ce dattawan yankin sun dukufa wajen ganin an warware matsalar.
“Mutane suna yin kuskure a kowani lokaci, mu mutane ne amma kuskure ba za a taba sanya shi ba a matsayin daidai. Don haka dole ne a nemo mafita.
“Tattaunawa da cikakkun bayanai a bainar jama’a yanzu bai zama dole ba, saboda an riga an yi wani babban yunkuri na warware rikicin. Wadanda ke da hannu a cikin yunkurin suna da himma sosai kuma suna iya aikin.
“Na yi imani da iyawarsu na nemo hanyar warware matsalar, kuma ina da kyakkyawan fata game da sakamakon lamarin. A wurina, babban abu mai muhimmanci shi ne, kawar zargi tare da tallafa wa tsarin don tabbatar da ci gaba. A nan ne hankalina ya karkata,” in ji shi.