Gwamnatin Jihar Kano ta soki matakin da ‘yansanda suka dauka na rufe kofar shiga fadar Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a ranar Juma’a.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Halilu Baba Dantiye, ya fitar, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ya haifar da tashin hankali da damuwa.
- Sin Ta Kafa Tasoshin Sigina Ta 5G Fiye Da Miliyan 4.1
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Nemi A Hukunta Jami’n Tsaro Masu Cin Zarifin Mata
Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnati na jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya tare da kira ga jama’a su kwantar da hankulansu tare da kauce wa yada jita-jita.
Rahotanni sun ce an rufe fadar ne don hana Sarkin tattaunawa kan batutuwan tattalin arziki, ciki har da sauya dokar haraji, da kuma nada sabon Hakimin Bichi.
Duk da haka, Sarkin ya samu damar gudanar da tarukan da ya tsara a cikin fadar gidan Rumfa.
Kokarin jin ta bakin ‘yansanda ya ci tura, amma garin Kano ya ci gaba da kasancewa cikin lumana, inda mutane ke ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.