Farfesa Kabiru Dandago, na Jami’ar Bayero da ke Kano, ya buƙaci gwamantin tarayya ta ƙara haraji ga masu kuɗi a Nijeriya maimakon ƙara harajin sayayya (VAT). A cikin wata hira da gidan talabijin na Trust TV a shahararren shirin Politics Today, Dandago ya yi kira ga gwamnati da ta gabatar da harajin kadarori, da harajin kayayyakin alatu, da haraji a kan hada hadar kuɗaɗen shiga, wanda zai iya ninka abin da ake samu daga VAT a yanzu.
Dandago ya bayyana cewa,
“Bana goyon bayan VAT ba kuma na ba da shawarar a cire shi. Gwamnati na iya samun kuɗaɗen daga harajin mu’amaloli, da harajin kayayyakin alatu, da harajin kadarori. Waɗannan ukun zasu iya samar da ninki biyu na abin da ake samu daga VAT.”
Ya ƙara da cewa waɗannan haraji na musamman za su taimaka wajen rage tazara tsakanin masu arziki da talakawa, domin masu kuɗi za su biya mafi yawa.
Ya jaddada cewa shiru da gwamnonin suka yi lokacin cire tallafin man fetur, wanda ya ƙara gaɓin kuɗi a rabon arziƙin ƙasa (FAAC), na nuna cewa adawar su ba ta haifar da jinƙai ga talakawa ba.