Gwamnonin da suka halarci taron ƙungiyar Gwamnoni ta Nijeriya (NGF) a Abuja a jiya Laraba, sun ƙi fitar da sanarwa ga manema labarai, wanda ya haifar da zarge-zarge game da ajandar taron da kuma sakamakon da aka samu.
Taron, wanda aka fara shi da karfe 10 na dare kuma ya ɗauki awa ɗaya, gwamnonin jihohi guda 15 ne suka halarce shi, ciki har da Alex Otti na jihar Abia, Chukwuma Soludo na jihar Anambra, da sauran gwamnonin jihohin Filato da Zamfara.
- Sanatocin Kudu Maso Gabas Sun Bukaci Duba Kudirin Dokar Gyaran Haraji
- Ma’aikacin Asibiti Ya Dawo Da Naira Miliyan 40 Da Aka Manta A Kano
Yawancin waɗanda suka halarci taron sun kasance mambobin jam’iyyar APC mai mulki. Sai dai wata al’ada mai ban mamaki, da ta faru, gwamnonin sun ƙi tattaunawa da manema labarai bayan taron kuma kowanne daga cikinsu ya tafi ɗaya bayan ɗaya.
Amma, wata majiya mai tushe ta bayyana cewa gwamnonin sun kasa cimma yarjejeniya kan dokokin sauye-sauyen haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gabatar a gaban majalisar tarayya.