Assalamu alaikum iyaye barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa a wannan fili namu me farin jini da albarka na Raino Da Tarbiyya.
A yau filin zai yi tsokaci ne a kan wayar hannu da ke hannun yaranmu. Shin mun taba tsayawa muka duba me yaranmu ke yi da wayoyin da ke hannunsu? Mun taba tsayawa muka duba da su wa suke mu’amala da wayar da ke hannunsu?
- Matsalar Tsaro: Masarautar Bichi Ta Gudanar Da Addu’o’i Na Musamman
- Da Ɗumi-ɗuminsa: Kwamishina Bunkasa Kasuwanci Da Masana’antu Na Jigawa Ya Rasu
Idan amsar ita ce a’a, hakika muna da babban aiki a gabanmu domin a yanzu wayar hannu babban kalubale ne ga tarbiyya da rayuwar yaranmu baki daya.
Mu sa ni waya ita ce hanya ta farko ta rugujewar tarbiyya cikin sauki ba tare da an sha wahala ba, da yawa iyaye kan yi hakin ko oho a lokacin da yara suka samu wayar hannu suke amfani da ita, yin hakan ganganci ne cike da hatsari.
A wannan zamani iyaye ba su iya raba yaransu da waya domin abin ya zama zamani idan yaronka ba shi da ita a hannu to abokinsa na da shi.
Za su kuma iya yin komai da ita ba tare da samun wata matsala ba.
Da waya ana iya yin zina da waya, ana iya yin damfara, ana iya yada duk wani na’uin aikin sharri da badala.
Yana da kyau mu sayi wayar da kanmu mu iyaye mu ba wa yaro, kuma muyi ta kula da sa ido a kan abin da suke yi da ita. Kar mu kyale su kara zube ya zama wayar ce ke sarrafa su ba mu iyaye da muka haife su ba.
Allah ya sa mu gyara ya kare mana zuri’a daga fadawa sharrin waya da zamani.