ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnatin Tinubu Na Amfani Da Kuɗaɗen Tallafin Mai Don Ci Gaban Al’umma – Minista

by Sulaiman
1 year ago
Tinubu

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur wajen aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa ƙarƙashin Shirin Sabunta Fata na Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Idris ya bayyana haka ne a Taron Shekara-shekara na Cibiyar Harkokin Jarida ta Duniya (IPI) na 2024 da aka gudanar a Abuja, wanda ke ɗauke da taken “Dimokiraɗiyya, ‘Yancin Kafofin Watsa Labarai, da Muhimmancin Kare Sararin Jama’a na Nijeriya.”

ADVERTISEMENT
  • Gwamnan Filato Ya Musanta Jita-Jitar Sauya Sheka Zuwa APC
  • Bayan Fara Aikin Matatar Mai Ta Fatakwal, Sai Kuma Me?

A cewar sa, ana amfani da kuɗaɗen tallafin da aka ajiye wajen shirye-shiryen da suka haɗa da bashin ɗalibai, gina ababen more rayuwa, bashi mai rahusa ga jama’a, bunƙasa aikin gona, da kuma shirin jinƙai na musamman.

LABARAI MASU NASABA

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Ya ce gwamnatin na mayar da hankali kan cigaban al’umma ta hanyar sauye-sauyen tattalin arziki da zuba jari domin samun cigaba mai ɗorewa ga al’ummar Nijeriya.

Ya ce: “Ana karkatar da tiriliyoyin Naira da aka rasa wajen shirye-shiryen tallafi marasa amfani zuwa manyan ajiyoyi, wanda hakan ke bai wa gwamnati damar saka jari a muhimman fannonin tattalin arziki.”

Ministan ya bayyana cewa gwamnatin na gudanar da sauye-sauyen tattalin arziki da suka shafi bunƙasa fannonin tattalin arziki, raya ƙwarewar ɗan’adam, da samar da cigaban tattalin arziki mai inganta kowa.

Ya ce babban abu a cikin waɗannan sauye-sauyen shi ne shirin haraji da aka gabatar wanda zai sauƙaƙa biyan haraji tare da rage wa talakawa nauyi.

“Ɗaya daga cikin abubuwan da suka ja hankali a wannan gyara shi ne sababbin kariya daga haraji da za su amfani mutane da kamfanoni da dama.”

Ya yi nuni da cewa waɗannan sauye-sauyen sun dace da manyan dabarun tattalin arziki, da tabbatar da samun dauwamammen sauyi da samar da Nijeriya mai gasa a duniya.

Idris ya kuma yi magana game da mayar da hankali na gwamnatin kan canjin makamashi, yana bayyana shi a matsayin muhimmin ɓangare na shirin cigaban Nijeriya.

Ya ce, “Shugaba Tinubu na jagorantar Nijeriya cikin wani sabon mataki na canjin makamashi, inda ya ƙaddamar da shirin shugaban ƙasa na canza ƙasar daga amfani da man fetur zuwa iskar gas ɗin da ake kira Compressed Natural Gas (CNG) a matsayin man motoci da injina.”

Wannan sauyi, inji shi, yana rage farashin sufuri zuwa kashi 60, da samar da ayyukan yi, da jawo jari mai yawa.

Game da kafofin watsa labarai, Idris ya tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu tana ba da muhimmanci wajen kare ’yancin kafofin watsa labarai da sararin jama’a.

Ya ce: “Tun lokacin da Shugaba Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayu 2023, mun sake jaddada aniyar mu ta tabbatarwa da faɗaɗa ‘yancin ‘yan jaridun Nijeriya.”

Sai dai, ya ja hankali cewa ’yanci ba shi da amfani idan babu sanin haƙƙi. Ya ce kafofin watsa labarai su kasance masu gudanar da muhawara mai amfani da kuma kula da hukumomi su ɗauki alhakin ayyukan su ba tare da tsananta wa masu ra’ayi mabambanta ba.

Idris ya ce: “Kowane ’yanci yana tare da sanin haƙƙi; ’yanci ba shi da ma’ana idan babu iyaka.”

Ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu yana ba da fifiko wajen gyaran tsarin shari’a domin tabbatar da kare haƙƙoƙin ɗan’adam, ciki har da ’yancin faɗar albarkacin baki da haɗin kai.

Ya bayyana gyaran a matsayin ginshiƙi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya da tabbatar da bin doka a Nijeriya.

A ƙarshe, Idris ya ce matakan da gwamnati ke ɗauka suna da matuƙar muhimmanci wajen gina Nijeriya mai arziki, inda ’yancin kafofin watsa labarai da alhakin ‘yan ƙasa ke taka muhimmiyar rawa wajen tsara tafiyar dimokiraɗiyya ta ƙasar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN
Labarai

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Next Post
Shugaban NPA Ya Kai Ziyarar Neman Masu Zuba Jari A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Onne Da Ta Jihar Ribas

Shugaban NPA Ya Kai Ziyarar Neman Masu Zuba Jari A Tashoshin Jiragen Ruwa Na Onne Da Ta Jihar Ribas

LABARAI MASU NASABA

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025
Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

Auren Da Ya Fi Auren Gidan Daula Dadi Ga Mace

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.