Mataimakiyar babban manaja a kamfanin harhada motoci na Sin wato Zonda Ghana Limited Fan Dongyun, ta ce motocin da kamfanin su ke harhadawa a kasar Ghana, na kara samun karbuwa tsakanin ‘yan kasar.
Fan Dongyun, wadda ta yi tsokacin yayin wani gangami na yabawa, da kwastomomin kamfanin suka gudanar a ranar Juma’a a birnin Accra, ta ce nau’o’in motoci da kamfanin ke harhadawa a Ghana, da suka hada da kananan motocin hawa, da na daukar kaya, da masu tafiyar nesa, da tifofin daukar kasa, da na hakar kasa, na cikin wadanda suka fi samun kasuwa a Ghana.
- Yau Ake Kece Raini Tsakanin Kungiyoyin Hamayya Na Manchester A Firimiyar Ingila
- Fahimtar Damammakin Da Sin Za Ta Samar Wa Duniya A Shekarar 2025 Daga Babban Taron Ayyukan Tattalin Arzikin Kasar
Jami’ar ta ce tun a watan Yunin bana, kamfanin ya shigar da nau’o’in motocin kamfanin “Great Wall” na Sin cikin kasuwar kasar, kuma cikin watanni 6 motocin sun yi matukar samun karbuwa a Ghana.
Daga nan sai Fan ta godewa gwamnatin kasar Ghana, bisa janye harajin VAT da ta yi kan ababen hawa da ake harhadawa a cikin kasar, wanda hakan ya sanya ‘yan Ghana ke iya sayansu yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)