Shafin Taskira shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacimmu na yau zai yi duba ne game da yanayin da muka shiga na sanyi. Ana yawan samun tashin gobara.
Usman Sani
A lokacin sanyi, yawan gobara yana yawaita ne saboda dalilai kamar haka:
1. Amfani da wuta don jin dumi. Mutane su kan kunna wuta don dumama jiki a gidaje ko wuraren aiki, ko majalisa wanda idan ba a kula ba, na iya haifar da gobara.
2. Amfani da kayan lantarki masu dumama daki: Na’urori kamar heater suna iya samun matsala idan an bar su a kunne na dogon lokaci. 3. Busawar iska: Yanayi na busawar iska da karancin ruwa a cikin iska na iya taimakawa wajen sa abu ya kama da wuta cikin sauri.
Saboda haka, ya zama wajibi mutane su kula da abubuwan da za su iya kawo gobara a lokacin sanyi.
Shatima Tijjani
Yawan samun wutar lantarki, da barin kayan wutar lantarki a kunne, mafi yawanci saboda kasalar jiki. Sannan a lokacin sanyi a kan samu matsalar rashin wuta, saboda kila an yi iska wuta ta lalace, idan aka kawo ta da karfi kuma kila an bar wani abu a kunne, to wannan shima yana kawo gobara sosai, sannan lokaci sanyi iska na kara rura wuta idan ta kama.
Sai kuma masu kunna irin wuta a kasko domin gida ko daki ya yi dumi, saboda a samu rage sanyi, mutane su dan ji dumi haka, to idan aka yi sakacin barin wuta aka kwanta bacci ko kuma an tura ta jikin labule ko gado, ba’a san sanda iska za ta zo ko ta daga labulen ya yi kan wuta ba kawai sai ya kama ko kuma iska ta hura wutar ta yi jikin gado sai ya kama, ga kuma iska tana hura nan da nan sai gobara ta tashi.
Sannan sai wani abu da shima ana sakacinsa, wato idan mata sun yi turaren wuta su kan bar kaskon turaren da wutar ba sa kashewa, to wannan shima iska tana iya rurawa ya yi sanadiyyar tada gobara a gida. Allah ya kara tsarewa.
Habiba Tijjani
Eh gaskiya ne yanayin sanyi ana samun gobara kam, sanyi yanayi ne da yake tafe da Iska, ita kuma Iska tana taimakawa wajen haddasa gobara, haka kunna maganin Sauro yana taimakawa saboda da duk yadda za’a rufe wurare dole dai sai an ji wannan sanyi ya buso Iska ta buso, to wannan iskar tana taimakawa wajen haddasa gobara ko in an yi girki a waje haka ga irin gidajenmu na gargajiya idan an yi girki da ice, idan ba’a kashe gawayi ba, idan lokacin zafi ne Iska ba za ta dauke wannan wutar ta kai ta wani wuri ba, amma lokacin sanyi da yake yana tafe da iska, za’a iya yin Iska mai kura da za ta dauki garwashin wuta ya fada cikin wani abu ko kuma ta dauko wani tsumma ta jefa shi cikin wutar.
To inda abubuwa zai iya taimakawa wajen hura wannan wutar to sai ka ga a nan ma gobara ta tashi. Ko idan an ajiye yayi a gidaje irin wannan yayin na abincin dabbobi ko dawakai, suma haka idan wuta ta shiga cikin su yana taimakawa wajen ta da gobara kuma duk sanyi ne yake bada gudu mawa.
A gaskiya sanyi yana bada gudunmawa sosai wajen haddasa gobara, ko ta bangaren wutar lantarki haka idan an kawo wuta da karfi to da dai sauransu.
Sannan yanayin sanyi kowanne makamashi na wuta a bushe yake sabanin lokacin damuna, ko wanne makamashi a bushe yake kamar jira yake a cinna masa wuta ya tashi da dai sauransu.