Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya sanar da ƙirƙirar sabbin masarautu bakwai domin haɓaka tsaro, zaman lafiya, da ci gaban jihar.
Sabbin masarautun sun haɗa da Huba a Hong, Madagali a Gulak, Michika a Michika, Fufore a Fufore, Gombi a Gombi, Yungur a Dumne, da Maiha a Maiha.
- Yawan Kai-Komon Mutane Tsakanin Lardunan Sin Zai Kai Kimanin Biliyan 64.5 A 2024
- ACG James Sunday Ya Yi Bikin Cika Shekaru 35 A Aikin NIS
Sarakunan Huba, Madagali, Michika, da Fufore za su kasance masu daraja ta biyu, yayin da Gombi, Yungur, da Maiha aka ba su daraja ta uku.
Gwamnan ya bayyana cewa ƙirƙirar masarautun zai ƙara inganta gudunmawar sarakuna wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jama’ar Jihar Adamawa.
Ya ce ire-iren waɗannan sauye-sauye su ne suke kawo sauyi mai tasirin gaske duba da yadda abubuwa suka lalace a tsakanin al’umma.
Ya ce yana sa ran sarakunan gargajiya su yi aiki tuƙuru wajen ganin sun haɗa kai a tsakanin al’ummarsu.